✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya kamata a yi kotunan hukunta masu garkuwa’

Kungiyar ACF ta nemi a yi kotunan musamman don hukunta masu satar mutane.

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta  gaggauta kafa kotuna na musamman domin yanke hukunci kan masu garkuwa da mutane.

ACF ta ce kotunan da za a kafan ne za su zama masu alhakin yanke hukunci a shari’ar masu aikata kisa da dillalan makamai da masu satar mutane da ’yan bindiga da dangoginsu.

Ta ce, “Ya kamata a hukunta masu laifi, masu gaskiya kuma a sake su, kamar yadda tsarin shari’a ya tanadar”; Shi ne abin da zai ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa gwamnati za ta yi wa tufkar hanci.

Shugaban Kungiyar, Cif Audu Ogbeh, ne ya yi kiran a cikin wani sako da ya fitar a lokacin ganawarsa da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo.

Ya ce, halin da ake ciki da bangare shari’a ya ki cewa uffan kan matsalar ce ta ba da damar yin, “Zargi da karairayin cewa ana sakin wadansu da aka kama ta bayan fage, saboda kabilanci ko bambancin addini.”

Audu Ogbe ya ce halin da Najeriya take ciki a yanzu ya fi kowane lokaci a tarihinta, bukatar hadin kai da yarda da juna, kasancewar kalubalen da kasar take fuskanta a yanzu ya fi na kowane lokaci.

“Yawaitar aikata manyan laifuka ta hana kowa barci. Matsalar tattalin arziki ta kara tsanani tare da haifar da damuwa da rashin tabbas a kasar,  wanda kuma ya haifar da mummunar rabuwar kai,” inji shi.