Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya ce lokaci ya yi da za a fara tafka muhawara kan batun sake fasalin kasa don kawo karshen kiraye-kirayen a ware na kabilanci a kasa baki daya.
Da yake jawabi a taron da bankin Union ya shirya a Legas, Sarkin ya ce tabbatar da zaman lafiya yana da muhimmanci ga al’umma da kasuwancin Najeriya saboda haka akwai bukatar gwamnati ta shigo cikin lamarin don kawo zaman lafiya.
Kundin tsarin mulkin kasar nan da ya ce wajibi ne kasar nan ta kasance akwai gwamnoni da masu taimaka musu a dukkan jihohi 36 da shugaban kasa da mataimakinsa da Ministoci daga kowace jiha da sanatoci fiye da 109 da ’yan majalisar wakilai da shugabannin kananan hukumomi 774 ba abu ne mai dorewa ba.