✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a kawo karshen siyasar kudi a Najeriya

Assalamu alaikum Edita; barka da aiki da fatan dukan ma’aikatanku suna cikin koshin lafiya. Ina yin kira na musamman ga ’yan siyasar Najeriya cewa ya…

Assalamu alaikum Edita; barka da aiki da fatan dukan ma’aikatanku suna cikin koshin lafiya. Ina yin kira na musamman ga ’yan siyasar Najeriya cewa ya kamata a yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen siyasar bayar da kudi a wannan kasa tamu.

Hakika siyasar bayar da kudi a runfunan zabe, tana matukar gurgunta kokarin da ake wajen ganin an samar da zabe mai sahihanci a wannan kasa. Yana da kyau a taka wa ’yan siyasa birkin amfani da baitul-malin gwamnati domin sayen masu kada kuri’a.  ’Yan siyasa suna amfani da talaucin da talakawa suke ciki wajen amfani da makudan kudade domin sauya tunanin masu kada kuri’a.

Babban kalubale ne ga dimokuradiyya a yi amfani da kudi wajen sayen kuri’un talakawa, duk da kiraye-kirayen da al’umma suke yi hadi da wasu kungiyoyi masu zaman kansu kan alfanun zaben dan takara nagari ba tare karbar kudi ba, amma abin takaici sai ranar zabe ka ga ana karbar kudi ana kada kuri’a ga mutanen da ba su cancanta ba, inda ake biyan masu bayar da kudi ana dangwala musu kuri’a.

Siyasar kudi ba za ka ta kai kasar nan ko’ina ba, domin dole ne duk wanda ya bayar da kudi aka zabe shi, idon ya kai inda yake kokarin kaiwa, ya cire abin da ya kashe kafin fara yi wa talakawa aiki.

Muna fatan Allah Ya kawo mana karshen siyasar bayar da kudi a Najeriya domin samun gyaruwarta.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, Dan Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa, Reshen Jihar Zamfara. 08133376020