✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya Kamata A Kafa Ma’aikatar ’Yan Bindiga da Makiyaya —Sheikh Gumi

Ya kamata gwamnati ta kula da ’yan bindiga irin kulawar da aka bai wa tsagerun Neja Delta

Fitacccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta kafa ma’aikata ta musamman domin kula da bukatun makiyaya da kuma korafe-korafen ’yan bindiga da suka addabi a sassan Najeriya.

Malamin ya bayyana cewa wajibi ne a bai wa al’ummar Fulani da sauran kabilu da yankunan Najeriya da ke da korafi kyakkyawar kulawar da ta dace kamar yadda aka yi wa tsagerun yankin Neja Delta.

“Ya kamata gwamnati ta fi bayar da muhimmanci ga wadannan mutane, saboda kullum abin da suke cewa shi ne suna da korafi.

“Abin da kawai nake so gwamnati ta yi musu, shi ne ta yi musu daidai da abin da ta yi wa matasan Neja Delta a lokacin da suke fasa bututan mai, suke gurgunta tattalin arzikin kasa.

“Su kuma wadannan mutane gurgunta harkar noma suke yi, wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasar nan.

“Abin daya kamata gwamnatin ta yi domin kare aukuwar wadannan abubuwa shi ne ta waiwaye su; akalla ta kafa Ma’aikatar Kula da Makiyaya wadda za ta rika lura da abubuwan da suka shafe su,” inji Sheikh Ahmad Gumi.

Ya bayyana haka ne a taron tsaro da makiyaya suka kira a ranar Laraba a Abuja, mai taken, “Lalubo hanyoyin zamani na magance matsalolin tsaro da ke addabar Fulani da makiyaya a Najeriya”.

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti (MACBAN) tare da Kungiyar Hadin Kan Arewa (NCM) ne suka shirya taron.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban Kungiyar MACBAN, Alhaji Husseini Bosso, ya ce matsalar garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga sun zama ruwan dare a cikin al’ummomi.

Bosso, ya ce sabanin yadda  ake zarin makiyaya da wadannan ayyukan ta’addanci, amma su matsalar ta fi shafa.

“Abin mamaki shi ne manyan laifuka da ake aikata wa manoma ba ya daukar hankalin kafofin  yada labarai, mambobinmu su suka fi kowa shan wahalar wannan matsala.

“Shugabannin MACBAN a jihohin Kogi da Neja da Nasarawa da wasau kanann hukumomin biyar na Abuja, ciki har da Gwagwalada, duk an yi garkuwa da su.

“Wannan ya kara tababtar da cewa babu wanda matsalar garkuwa da mutane ’yan bindiga ta bari,” inji shi.

A cewarsa, daga 2015 zuwa yanzu, an kashe makiyaya da dama, wasu sama da miliyan biyu kuma sun tsere daga muhallansu a sakamakon matsalar tsaro.

A gefe guda kuma, dabbobinsu da gwamnati ko ’yan bindiga suka kwace sun haura guda miliyan hudu.

Bosso, ya yi tir da abin kisan rashin imani da kungiyar IPOB take yi wa makiyaya, yana mai cewa ya zama jazaman ta daina.

Ya kuma bayyana damuwa cewa gwamnati ba ta bayar da diyya ko matsuguni ga makiyayan da bata-gari suka kwace wa dabbobi.

“Duk da haka ba a ba su matsuguni ko diyya kamar yadda ake wa sauran ’yan Najeriya da irin haka ta faru da su. duk da cewa su ba su da wata sana’a ko kware, wanda hakan babban hadari ne.

%d bloggers like this: