✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a haramta sayar da magani a kan tituna – Hajiya Talatu

Hajiya Talatu Uwa Ebune kwarariya ce mai digiri na biyu kan ilimin Hada Magunguna, wadda ta shahara wajen harkar kasuwancin magunguna da sauransu. A wannan…

Hajiya Talatu Uwa Ebune kwarariya ce mai digiri na biyu kan ilimin Hada Magunguna, wadda ta shahara wajen harkar kasuwancin magunguna da sauransu. A wannan tattaunawar da Aminiya, ta yi karin haske game harkarsayar da magani da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ya kika fara wannan sana’a ta saye da sayar da magunguna?
Hajiya Talatu: Sunana Talatu Uwa Ebune, an haife ni a garin Jos, a ranar 23 ga watan Nuwamban shekarar 1965. Ni ’yar kabilar Igala ce daga karamar Hukumar Ankpa ta Jihar Kogi. Na yi makarantar mishan na Ankpa sannan na wuce makarantar kwana ta Talatar Mafara. Daga nan sai na yi karatu har matakin diploma a ilmin hada abinci masu gina jiki. Sai kuma maigidana ya yi ta maza ya yarje mini da in je in ci gaba da karatu, sai na samu damar shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), inda a nan ma na karanta ilmin hada magunguna amma a matakin digri.
Aminiya: A wane wuri kika fara aiki?
Hajiya Talatu: Na fara aiki da Hukumar Kula da Abinci da Tantance Magunguna ta kasa wato NAFDAC. Sannan na koma jami’ar ABU da aiki na kuma Osbud-K Pharmacy. Daga baya na ci gaba na yi digiri na biyu duk dai a jami’ar ABU. Kafin daga baya na kafa tawa kantin na hada magunguna da ake kira NANA.
Aminiya: Me ye ja ra’ayinki kan koyon ilimin harhadawa da sayar da magunguna?
Hajiya Talatu: Tun ina karama ina shawar aikin jinya. Daga baya naga na fi son hada wa da sayar da magani. Bugu da kari, wacce ta rike ni malamar asibiti ce. Sannan akwai ’yan ajin mu da suka kara mini kwarin gwiwa irinsu Hajiya Asabe Sule daga Jihar Sakkwato da dai sauransu. Muna haduwa a taron kara wa juna ilimi na shekara-shekara.
Aminiya:Wadanne kalubale kika fuskanta lokacin karatu?
Hajiya Talatu: Lallai duk abin da ka dage za ka iya ganin bayansa. Maigidana da ’ya’yana sun taimaka mini matuka. Amma ba cika baki ba. Karatun aikin hada magunguna bana raggo ko ragguwa ba ce, don ba ka da lokacin wasa, sai dai ina kafito karatu, ina za ka karatu. Idan ana ruwa, ko tsananin zafi dole ne kaje karatu. In har malami zai je aji da karfe bakwai na safe ran Lahadi, waye kai ka ki zuwa aji. Ba mu da lokacin sa janbaki, ko hoda.
Aminiya: Wadanne malamanki za ki iya tunawa da su?
Hajiya Talatu: Tsohon Shugaban Jami’a Farfesa Abdullahi Mustapha, Farfesa Ilyas da kuma Bhatiya wadanda Ba’indiye ne, Onalapo da kuma MG Garba.
Aminiya: Akwai bambanci tsakanin mai ilimin hadawa da sayarda da magunguna da kuma dillalin magunguna?
Hajiya Talatu: Mai ilimin harhada magunguna yana da alamar Rd a kofar shagon sa, yana sanya farar rigar Jaket a kan kayansa, sannan ba ya sai da magani mai karfi, sai ya ga takardar likita. Inda shi kuma dillali mai neman na tuwo bashi da daman sa wannan alama. Ba zai iya saye da sayar da magani mai karfi ko mai hadari ba. Sannan yana iya wanke ciwo ya sa magani kafin a je ganin likita a asibiti.
Aminiya: Me ye ra’ayinki kan yadda ake yawo ana sayar da magani a kafada?
Hajiya Talatu: Hakan bai dace ba. Kuma yana tattare da hadari sosai. Najeriya ba ta kula sosai da hadarin shan maganin da ya sha rana. Hada-hadar magani ba ta jahili ba ce.
Aminiya: Ta wace hanya za a magance hakan?
Hajiya Talatu: Ba aikin mutum daya ba ne. Ya dace kowa ya ba da gudunmuwarsa. Amma idan ba mai saye, ba za a sami mai talla ba. Kuma ya dace jama’a su guji sayen magani a kan tituna. Kuma hukumomin gwamnati irinsu NDLEA da NAFDAC su kara himma. Ya kamata a haramta sayar da magani a kan tituna. Kuma idan masana kadai ke cinikin magunguna, to ba za a sami masu sayar wa ’yan kwaya ba. Sannan ya dace a rinka hukunta masu karya doka.
Aminiya: Me ye ra’ayinki, don a kwanaki an hana sayar da magani a kan titi a Kano, an kuma ce sai mai ilimi zai yi harkar?
Hajiya Talatu: Ya kamata duk jihohi su kwaikwayi haka. Ya dace a san kamfanin da ake hadawa da sayar da magani. Ba kawai a yi a bayan gida ba, a sayar a kan titi. Ana iya cewa magani na da hadari, a dawo da shi, ina kamfani ne an san wanda ya sa ya, sai a dawo da shi. Amma idan a kan titi ne ai shiru za ka ji.
Aminiya: Ta ya ake hukunta masana da suke hulda da jabun magunguna ko harka da ’yan kwaya?
Hajiya Talatu: Duk masani mai lasisi yana tsoron a janye masa lasisi. Akwai hukumar kula da masana ilimin hadawa da sayar da mugunguna. Kuma duk wanda aka kama ba za a raga masa ba. Amma dillalin magani a kafada ba su da mai hukunta su don haka suke cin karensu babu babbaka.
Aminiya: Me za ki ce game da batun cewa kasar nan ba ta hada magunguna ingantattu?
Hajiya Talatu: Ba haka ba ne. Muna da kamfanoni masu hada mugunguna nagari.
Aminiya: Me ya sa idan an horar da masani a kasar nan, sai kasashen ketare su dauke shi su ba shi aiki?
Hajiya Talatu: Ba wurin da ya fi gida. Don duk inda kake ba kasar ka ba, to kai a baya kake. Ya dace a samar da kayan aiki, da wutar lantarki don mu jagoranci Afirka ta Yamma.
Aminiya: Me ye illar shan magani ba tare da izinin likita ba?
Hajiya Talatu: Kada wanda ya sha magani ba tare da izinin likita ba. Don akwai maganin da ban son in fadi sunansa don an yi ne saboda wani abu daban, amma ’yan kwaya sun mayar da shi don wani abu mai sa su yin maye. Bai dace ba mutum ya dauki kudin shi ya lahanta lafiyarsa.
Aminiya: Ko kina da magada?
Hajiya Talatu: (Dariya). dana na fako ya fara karatun hada magunguna ya bari. Yanzu ya kammala karantun kwamfuta. ’Yata kuma ta karanta fannin tsimi da tanaji ne.