✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kamata a dauki matakin bai wa ’yan jarida kariya a filin daga —ICRC

Kungiyar ba da Agaji ta Kasa da Kasa (ICRC) ta yi kira da a gaggauta daukar matakin ba da kariya ga ’yan jarida da ke…

Kungiyar ba da Agaji ta Kasa da Kasa (ICRC) ta yi kira da a gaggauta daukar matakin ba da kariya ga ’yan jarida da ke aiki a wuraren da ake gwabza fada.

Jami’in Hulda da Jma’a na kungiyar, Mista Aliyu Dawobe ne ya yi wannan kira a wajen taron kara wa juna ilimi na yini biyu da aka shirya a Kano ranar Juma’a.

Taron ya maida hankali ne kan abin da ya shafi ’yan jarida da masu aikin jinkai da ke aiki a wuraren da ake fama da tashin-tashina.

Dawobe ya ce galibin ’yan jaridar da ke aiki a wuraren da ake fama da rikice-riki su ma rikicin kan rutsa da su a karshe.

Don haka ya ce wajibi ne a bai wa ’yan jarida kariya da kuma martaba su yayin da suke bakin aiki a ire-iren wadannan wuraren.

Ya kara da cewa, duba da yanayin akin ’yan jarida a fagen yaki, yayin da sauran jama’a ke tserewa don neman mafaka, su kuwa kokarin kutsawa suke yi domin sanar da al’umma gaskiyar abin da ke faruwa.