✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martinez Zogo: An tsinci gawar dan jaridar Kamaru da aka sace

An dade ana zargin gwamnatin Paul Biya da murkushe ‘yan adawa.

An tsinci gawar wani fitaccen dan jaridar kasar Kamaru da aka daddatse a ranar Lahadi a kusa da birnin Yaounde, kwanaki biyar bayan da wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da shi, a cewar kungiyar ’yan jarida da wani abokin aikinsa.

Masu fafutukar kare ‘yan jarida sun bayyana bacewar Martinez Zogo da mutuwarsa a matsayin wata alama da ke kara nuna hadarin da ke tattare da aikin jarida a kasar ta Afirka.

Zogo, wanda shi ne daraktan gidan rediyo mai zaman kansa na Amplitude FM, a ranar 17 ga watan Janairu wasu da ba a san ko su waye ba suka yi garkuwa da shi bayan da ya yi kokarin shiga wani ofishin ‘yan sanda domin tsere wa maharan, kamar yadda kungiyar sa ido kan kafafen yada labarai ta RSF ta bayyana.

A baya-bayan nan Zogo ya yi ta magana ta rediyo game da wani batun almubazzaranci da ya hada da wata kafar yada labarai mai alaka da gwamnati, in ji RSF.

“Kungiyar ‘yan jaridan Kamaru ta rasa daya daga cikin mambobinta, a cewar kungiyar rajin ‘yan jarida ta Kamaru a cikin wata sanarwa.

“Ina ’yancin aikin jaridar yake, da ’yancin bayyana ra’ayi, da ’yancin fadin albarkacin baki a Kamaru idan har aiki da kafafen yada labarai a yanzu na tattare da hadari?”

Abokin aikin Zago, Charlie Amie Tchouemou, babban editan gidan rediyon Amplitude FM, ya tabbatar da sace Zogo da mutuwarsa.

Sai daga majiyoyo da dama a kasar sun ce har yanzu ’yan sanda da gwamnati dai ba su ce komai ba kan batun.

Wannan lamarin shi ne na baya-baya da ake kai wa ‘yan jarida a kasar Kamaru hare-hare, kasar da ke da ‘yan jarida masu hazaka wadda kuma Paul Biya ke shugabanta.

An dade ana zargin gwamnatin Shugaba Biya da murkushe ‘yan adawa, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Reuters.

Kasar Kamaru na daya daga cikin kasashe da dama a nahiyar Afrika, kama daga Burkina Faso, zuwa Habasha da Equatorial Guinea, inda ’yan jarida ke korafin cewa ’yancin aikin jarida na fuskantar barazana daga gwamnatocin kama-karya.