✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Ya kamata a ayyana dokar ta-baci a fannin lafiyar Najeriya —Likitoci

Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta nuna damuwa kan yadda kwararrun likitocin kasar ke ficewa zuwa ketare yin aiki

Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta-baci a fannin lafiyar kasar.

NMA ta ce bukatar ayyana dokar ta taso ne duba da yadda wasu cututtuka, ciki har da zazzabin lasa da COVID-19 da sauransu ke ci gaba da yi wa lafiyar ’yan kasa barazana.

Shugaban NMA na kasa, Dokta Omosehin Adeyemi-Osowe, ya ce, don haka ya ce, “Muna kira ga gwamnatocinmu da su hanzarta ayyana dokar ta-baci a fannin lafiyar Najeriya da daukar matakan da suka dace don amfani ‘yan kasa.”

Likitan ya yi kiran ne yana mai nuna damuwarsa kan yadda kwararrun likitocin Najeriya suke yin kaura zuwa ketare da aiki.

Ya ce a halin da ake ciki, baya ga kasashen Indiya da Pakistan, Najeriya ce kan gaba wajen yawan likitoci masu aiki a kasar Birtaniya.

Ya bayyana haka yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a wajen wani taro a Akure, Jihar Ondo.