✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kafa tarihin zana nau’o’in kwari 864 a jikinsa

Guinness World Records ya tabbatar da shi a wanda ya kafa tarihin yin jarfar mafi yawan kwari

Wani mai suna Michael Amoia dan asalin Jihar New York da ke Amurka ya samu lambar yabo ta Kundin Tarihi na Duniya ta hanyar yin jarfa na kwari 864 a jikinsa, inda ya nuna wani abin da ba a zata ba game da kansa: Sai dai ya ce, “Ina kin kwari.”

Guinness World Records ya tabbatar wa Michael Amoia kambin wanda ya kafa tarihi na yin jarfar mafi yawan kwari da aka zana ta hanyar yin tattoo a jikinsa, inda aka kididdige jarfa a hukumance ta kai 864.

Amoia ya dauki ragamar wannan Kambin Tarihin ne daga wani dan Birtaniya mai suna Badter Milsom, wanda aka yi wa zanen kwari 402 a jikinsa.

Amoia, wanda aka yi wa zanezanen, ya fara ne da wata sarauniyar tururuwa da aka yi wa tawada a hannunsa tun yana dan shekara 21, ya ce sau da yawa mutane sunakuskuren cewa, yana son kwari.

“Yawancin mutane suna tunanin ina son kwari – a zahiri, amma sabanin hakan ne. Ina jin tsoron kwari, ina kin kwari. Amma zanen yana da ma’anoni da yawa, shi ya sa na sanya su a jikina duka,” Amoia ya shaida wa jami’an Guinness.

Ya ce, “Zanen na nuna wata ma’ana ne mai duhu, amma akwai karin sako mai inganci.”