✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya guntule hannun maƙwabcinsa kan neman matarsa

Wani magidanci ya guntule hannun maƙwabtacinsa, ya kuma sare shi a goshi kan zargin kwanciya da matarsa.

Wani magidanci ya guntule hannun maƙwabtacinsa, ya kuma sare shi a goshi kan zargin kwanciya da matarsa.

Bayan ya yi wanda yake zargi da kwartancin aika-aika ne Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kwara ta gurfanar da shi kotu.

Dan sanda mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, ya shaida wa kotun majistare cewa dan uwan wanda aka file wa hannun ne ya kawo musu karar abin da ya faru a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta jihar.

Takardar tuhumar da aka karanta masa a kotun ta ce, “Ana zargin kan da saran sa da adda a goshi da kuma file masa hannunsa na dama a yayin dawowa daga Kasuwar Kara.

“Ka kuma bayyana cewa kana zargin sa da neman matarka, kuma ka sha kama su suna aikata masha’a

“Ka ce ka gan shi yana magana da ita, amma daya hango ka sai ya tsere kafin ka far masa.”

Daga nan sai mai gabatar da kara ya bukaci kotun ta tsare magidancin, kuma ta amince.

Alƙalin kotun, Gbadeyan Kamson, ta dage shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Oktoba, 2023.