✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya gudu da budurwar mahaifinsa mako uku kafin daura musu aure

Ya ce zai auri yarinyar su hayayyafa kafin ya dawo gida.

Wani matashi mai suna Ahmed Golo mai shekara 24 ya gudu da wata budurwa mai suna Sa’ada Mohammed mai shekara 18 a duniya da mahaifinsa Ishmael Golo mai shekara 71 yake shirin ya aura bayan Sallah da mako daya, inda ya ce budurwar ta yi wa mahaifinsa nasa yarinta.

Lamarin ya auku ne a kauyen Magarjali da ke Gundumar Tana Riber a kasar Kenya kamar yadda jaridar The Nation ta Kenya ta ruwaito a ranar Alhamis din makon jiya.

Wani daga cikin ’yan uwan Mista Golo mai suna Hassan Wario ya ce, dattijon ya riga ya shirya da budurwar har ya biya sadakinta, inda aka yanke shawarar daura musu aure a bayan azumi.

Ya amince shi da iyayen budurwar cewa a bar bikin aurensu sai bayan Karamar Sallah da mako daya, amma sai ’ya’yansa suka turje suka ce matar da zai aura ba ta kai autarsa a shekaru ba, don haka suka nemi ya sake shawara.

Mista Wario ya ce duk kokarin da aka yi don shawo kan ’ya’yan Mista Golo su amince da zabin mahaifinsu ba a cim ma nasara ba, wanda hakan ya jawo takaddama a cikin iyalan.

Ya ce, “Mun yi kokarin jawo hankalinsu amma suka ki. Hatta mahaifiyarsu ta yi kokarin kwantar musu da hankali amma suka yi kunnen kashi, musamman ’ya’yansa mata.”

Bayan kasa shawo kan ’ya’yan ne sai babban dan matarsa ta biyu ya yanke shawarar gano inda amarya mai jiran ranar take, inda ya gudu da ita.

A ranar Talatar makon jiya da mutane suke kokarin zuwa masallaci ne Ahmed da Sa’ada suka gudu inda suka bar rubutaccen sako ga mahaifinsa suna ba shi shawarar ya nemi mace daidai da shi ya bar kananan ’yan mata ga ’ya’yansa maza.

“Da misalin karfe 10 na safe ne muka fahimci ba ta nan, saboda ba mu gan ta ba, sai muka gano wani rubutu da harshenmu amma ba rubutunta ba ne,” in ji ’yar uwar Sa’ada mai suna Asha Fadhe.

Washegari Laraba, Ahmed ya kira gida ya yi magana da mahaifiyarsa ya shaida mata cewa ba zai bari mahaifinsu ya zubar da mutuncin gidansu ba.

Mahaifiyar ta ce Ahmed ya ce lokacin da tsofaffi za su rika auren jikokinsu ya wuce, inda ya bukaci mahaifinsa ya nemi wata madaidaiciya ya aura.

“Ya ce, zai auri yarinyar su hayayyafa kafin ya dawo gida. Na yi kokarin shaida masa hakan bai dace ba, amma ya ce budurwar ta yarda kuma yana farin ciki ya kubutar da ita,” in ji ta.

Iyalan gidan su Sa’ada sun ce ta sanar da su cewa tana nan lafiya. Sun ce ta shaida musu cewa, ba ta son auren Mista Golo inda ta ce ya yi mata tsufa kuma zai fi kyau ta auri matashi.

Sai dai Mista Golo ya zargi uwargidansa da matarsa ta uku da tunzura ’ya’yansa su ki amincewa da auren nasa, inda ya ce su ne suka kisa wannan badakala.

Tuni ya bukaci iyayen budurwar su dawo masa da sadakinsa, inda ya ce sai su je su nemi sabon sadaki a wajen dansa.