Wani magidanci dan kasar Indiya ya karrama matarsa ta hanyar gina mata gida mai kama da fitaccen gidan nan na Taj Mahal.
Mutumin, wanda malamin makaranta ne mai suna Anand Prakash Chouksey, ya ce an shafe shekara uku ana ginin gidan Madhya Pradesh da ya gina a matsayin kyauta ga matarsa, mai suna Manjusha mai shekara 48.
“Kyauta ce ga matata, amma kuma ga garina da jama’ar garin,” inji Chouksey mai shekara 52.
Ya ce, ginin gidan ya ci kimanin Dalar Amurka dubu 260 (kimanin Naira miliyan 140), inda aka gina shi bisa taswirar katafaren gidan na Taj Mahal, wanda aka yi a Karni na 17 a birnin Agra da ke kusa da Kogin Yamuna a kasar Indiya, wanda yanzu ya zama abin al’ajabi a duniya.
Chouksey ya ce, da farko yana son kwaiwayon ginin Taj Mahal ya kai tsawon kafa 80, amma ya yi watsi da umarnin hukumomin yankin tare da rage shirinsa na ganin gidan zuwa kafa 29.
Chouksey ya ce, daga wajen gidan ya dogara ne a kan nau’in ginin Taj Mahal, amma cikin gidan yana da karin tsari na zamani.
Yayin da masu fasaha daga West Bengal da Indore suka taimaka da fafe cikin gidan, masu sana’ar kira daga birnin Mumbai ne suka kera kujeru da sauran kayan daki na gidan.
Sarkin Mughal Shah Jahan ne ya gina ainihin gidan Taj Mahal don gina kabarin matarsa Mumtaz Mahal a 1632 Miladiyya.