✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya gargadi dalibai kan shiga kungiyoyin asiri

Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Muhammad Tanko ya gargadi sababbin daliban da jami’ar ta dauka su guji satar jarrabawa ko shiga kungiyoyin asiri da…

Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Muhammad Tanko ya gargadi sababbin daliban da jami’ar ta dauka su guji satar jarrabawa ko shiga kungiyoyin asiri da duk ayyukan da ka iya sanyawa a kori dalibi daga makaranta ba tare da la’akari da matakin karatunsa ba.

Farfesa Muhammad Tanko, wanda Mataimakin Shugaban Jami’ar (Sashin Gudanarwa), Farfesa Yohanna Tella ya wakilta a wajen bikin rantsar da sababbin daliban shekarar 2019/2020 da aka gudanar a tsangayar jami’ar da ke Kafanchan, ya ce babu ruwan jami’ar da nuna sani ko sabo ga duk wanda ya keta huruminta. Ya ce, “Duk wanda muka kama da daya daga cikin laifuffukan da muka zayyana za mu kore shi daga jami’ar ba tare da la’akari da matakin karatun da yake ba.”

Sai ya yi kira ga daliban da kada su ba iyayensu da suka sadaukar da abin da suka mallaka don ganin sun samu ilimi mai inganci kunya, ko sauran al’ummar kasa da suka dogara gare su a matsayin manyan gobe.

“Wannan makaranta ta yaye zakakuran dalibai da dama da a yanzu haka wadansunsu da dama na rike da manyan mukamai a bangarori daban-daban na kasar nan,” inji shi.

D yake jawabin tunda farko, Shugaban Tsangayar Jami’ar ta Kafanchan, Farfesa Ado Baba Ahmed ya ce sun fara karatu a tsangayar ce a shekarar 2012 da daliban da ba su haura 200 ba, amma zuwa yanzu har rasa damar daukar wadansu daliban suka yi saboda karuwar dalibai da kuma rashin isasshen gurbi a makarantar.

Ya gargadi daliban su guji dukkan munanan ayyukan da za su kai ga korarsu daga makaranta musamman ayyukan kungiyoyin asiri da satar jarrabawa, inda ya bada misalin dalibai 80 da jami’ar ta kora wadanda 10 daga ciki sun fito ne daga  jami’ar da ke Kafanchan.

Fiye da dalibai 4,650 Jami’ar Jihar Kaduna ta dauka inda sama da 700 daga ciki za su yi karatu ne a harabar jami’ar da ke Kafanchan.