✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya dawo gida bayan ‘bacewarsa’ da shekara 65

Malam Sa'idu ya bar gida tun kafin Najeriya da samu ’yancin kai.

Wani mutum da aka sanar da bacewarsa kimanin shekara 65 da suka gabata a garin Dakatsalle na Karamar Hukumar Bebeji, Jihar Kano, ya dawo gida.

Tsohon ya bar garin na Dakatsalle ne tun yana shekara 20, tun daga lokacin babu wani dan uwansa da ya kara ganin sa, lamarin ya sa mutane suka cika da mamakin dawowarsa.

  1. ’Yar shekara 37 ta haifi jarirai 10 lokaci guda
  2. Yunwa ta sa daliban sakandare zanga-zanga a Gombe

Mazauna garin na ta tururuwar ganin dattijon da ya safe wadannan shekaru rabonsa da gida, har an debe tsammanin yana nan a raye saboda neman sa da aka sha yi ba tare da an dace ba.

Mutumin mai suna Malam Sa’idu Abdullahi ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa ya bar gida ne tun zamanin mulkin Sarkin Kano Abdullahi Bayero, kaka ga sarki mai ci Aminu Ado Bayero, tsakanin 1926 zuwa 1953.

Katin shaidar dan kasa ya nuna Malam Sa’idu yana da shekara 73 a duniya, amma bayanan batarsa sun nuna yana shekarunsa sun haura 90 a duniya.

Datttijon ya ce kokarin bunkasa kasuwancinsa na goro ne ya sa shi zuwa Kudu tun da kuruciyarsa a wancan lokaci, inda ya koma birnin Ibadan na Jihar Oyo, ya yi ta rayuwa har zuwa tsufa.

Ya ce ya jima yana son dawowa gida cikin ’yan uwansa da ya bari tun kafin Najeriya ta samu ’yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Duk da shafe wadannan shekaru a kasar Yarabawa, har yanzu karin harshen Malam Sa’idu bai sauya daga na Bahaushe ba.

Tuni dai ’ya’yan ’yan uwa da na makwabta suka shiga murnar dawowar dan uwan iyayensu da ba su taba gani ba, yayin da wasu ’yan uwansa ke cewa har sun manta da kammaninsa.

Dubban mutane na ta rige-rigen ganin dattijon da ya bar kauyen Damau tun kafin kafuwar Jihar Kano, a lokacin turawan mulkin mallaka.