✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya datse hannuwan mahaifiyarsa da adda saboda rashin jituwa

Wani matashi ya datse hannuwan mahaifiyarsa mai shekaru 65, ya kuma sassare ta a kanta da sauran sassan jikinta kan sabanin da suka samu

Jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai shekaru 30 da ya sare hannuwan mahaifiyarsa da adda saboda rashin jituwa.

Shaidu sun ce matashin ya kuma yi wa mahafiyar tasa mai shekaru 65 mummunan sara a kanta, sannan ya yayyanke ta a kafarta da wasu sassan jikinta.

Wanda ake zargin ya yi wa datijuwar wannan aika-aika ne a kauyne Akibo da ke Karamar Hukumar Obafemi Owode ta Jihar Ogun.

A cikin daren ranar Laraba ne aka ji hayaniya a gidan tsohuwar, inda makwabta suka je domin kai dauki, amma ko da suka isa,  sai suka same ta cikin jini, da hannuwanta biyu duk an datse su, da kuma sara a kanta, shi kuma dan nata yana tsaye a kanta ya rike wata sharbebiyar adda.

Jaridar Punch ta ruwaito wani makwabcinsu yana cewa wanda ake zargin ya kuma sari mahaifiyar tasa a kafa da wasu sassan jikkinta, amma an kai ita asibiti domin ba ta kulawa.

PUNCH Metro ta ruwaito kakakin yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, na tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce  rundunarsu ta cafke matashin kuma rundunar na gudanar bincike kan lamarin.