✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace gwamnati ta tallafa wa harkar fim don samar da aikin yi – Musa Mudi

Alhaji Musa Mudi shi ne babban jami’i da ke kula da shiyyar Kano, a Hukumar Kula da Al’amuran Fina-finai ta Najeriya. A tattaunawar da ya…

Alhaji Musa Mudi shi ne babban jami’i da ke kula da shiyyar Kano, a Hukumar Kula da Al’amuran Fina-finai ta Najeriya. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya bayyana ayyukan hukumar, tare da ba da tabbacin cewa idan gwamnati ta tallafa wa harkokin shirya fina-finai a Najeriya, miliyoyin matasa za su samu ayyukan yi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mene ne ayyukan hukumarku game da shirya fina-finai a Najeriya?
To, ita dai wannan hukuma mai kula da al’amuran fina-finai ta Najeriya, wadda babban ofishinta yake garin Jos, tana karkashin Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu ta Najeriya ce, kuma an kafa dokar da ta kafa ne a 1979. Daga baya aka bude ofisoshin shiyya na hukumar a Kano da Legas da kuma Abuja. Ayyukan wannan hukuma su ne kula da ci gaban shirya duk wasu fina-finai, kamar fina-finan tarihi da fina-finan walwala da nishadi da duk abubuwan da suka shafi inganta shirya irin wadannan fina-finai. Aikinmu ne mu sanya ido, mu tabbatar cewa ana bin tafarkin da ya dace da al’adunmu da zamantakewarmu, wajen shirya irin fina-finan.
Ta wadanne hanyoyi ne kuke gudanar da ayyukanku, musamman a Kano?
To, kowa ya san yadda Kano ta yi suna kan harkar shirya fina-finai a kasar nan. Bayan Kano akwai Kaduna da Sakkwato da ke karkashin wannan shiyya a ofishin wannan hukuma. Hanyoyin da muke bi wajen gudanar da ayyukanmu su ne, muna sa ido kan yadda ake shirya fina-finai a shiyyar Kano. Saboda fina-finan da ake shiryawa a  shiyyar sun bambanta da wasu fina-finan da ake shiryawa a kasar nan, a bangaren al’adu.
Kuma kamar yadda na fada ne, yadda muke gudanar da ayyukanmu su ne, duk inda za a tallafa wa wani ma’aikacin shirya fim kan maganar ilimantarwa da sa shi a hanya, da ba shi gudunmawa, muna yi. Kuma muna ba su shawarwari kan inganta shirya fina-finai a wannan shiyya, ta hanyar shirya musu tarurrukan kara wa juna sani, a inda muke tattaunawa kan abubuwan da za su inganta harkokin shirya fina-finai. Bayan haka muna da makaranta ta musamman kan shirya fina-finai a garin Jos, wadda muke horar da masu shirya fina-finai saboda muhimmancin wannan sana’a. Domin kowa ya san harkar fim, sana’a ce da take taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan, tare da samar da ayyukan yi ga dubban matasa.
Akwai shirye-shirye da shugaban hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ya kawo, wanda muka hada hannu muke aiki tare, don ilimantar da masu shirya fina-finai a jihar.
Muna da burin mu fadada ayyukanmu zuwa sauran jihohin da ke karkashin wannan shiyya, kamar Kaduna da Katsina da Jigawa da Gombe da sauran jihohin Arewa.
Ganin irin rashin aikin yi da ake fama da shi a kasar nan, wace gudunmawa ce kake ganin shirya fina-finai zai kawo wajen samar da aikin yi a Najeriya?
Kamar yadda na fada ne a baya, sana’ar fim tana samar da ayyukan yi a kasar nan, domin tsakani da Allah ba ya ga sana’ar noma babu sana’ar da take samar da ayyukan yi a kasar nan kamar sana’ar fim. Don haka lallai ne ya kamata gwamnati tallafa wa wannan harka. Babu shakka wannan bangare na shirya fina-finai yana daga cikin abin da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kula da shi. Idan gwamnati ta sanya kudi a wannan harka, za a samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar nan. Kuma idan gwamnati ta sanya kudi a wannan harka, za ta samu damar sanya idanu kan yadda ake gudanar da wannan harka.
Bayan kasar Indiya da Amurka, Najeriya ita ce ta uku a duniya wajen shirya fina-finai kuma kasuwar fina-finai ta Najeriya ba wai ya tsaya a gida ne kadai ba. Duk kasashen da suke makwabka da Najeriya, kamar Ghana da Nijar kai har Saudiyya, duk ana kai fina-finan Najeriya. Saboda haka idan gwamnati ta shigo wannan harka ta tallafa, masu shirya fina-finai za su samu gagarumar nasara.
A karshe, wane sako ko kira kake da shi zuwa ga masu wannan sana’a ta fim?
To, shawarata ga masu wannan sana’a ita ce, su kara kokari su ilimantar da kansu kan wannan sana’a kuma su hada kai da mu. Ba fadace-fadace, kungiyoyin masu shirya fina-finai ya kamata su rika yi ba. Don Allah su hada kai, idan suka yi haka za su taimaki kansu da kansu.