✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya dace gwamnati ta sake gina kasuwar Kafanchan’

An bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna da ta taimaka ta sake gina tsohuwar kasuwar garin Kafanchan da aka kona lokacin rikicin zaben shekarar 2011.Sabon shugaban ‘yan…

An bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna da ta taimaka ta sake gina tsohuwar kasuwar garin Kafanchan da aka kona lokacin rikicin zaben shekarar 2011.
Sabon shugaban ‘yan kasuwan garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Alhaji Salisu Idris ne ya yi wannan kiran, a lokacin da yake ganawa da Aminiya.
Shugaban ya ce duk da dai ya san wanna gwamnati ba ta da kudi a yanzu haka, amma lura da irin muhimancin da kasuwar take da shi da kuma irin kudin shigar da gwamnati ke samu, sannan kuma wannan ita ce babbar kasuwar yankin kudancin Jihar Kaduna, wadda ta hada manyan kabilu daban-daban, yana da kyau a ce an gyara ta.
Da ya waiwayo ga sabon matsugunin da kasuwar ke ci yanzu, ya ce suna da ‘yan matsalolin da su ke bukatar gwamnati ta yi musu magani. Ya ce “matsalolin sun hada da fitar da hanyoyin ruwa wanda rashinta ya addabar kasuwar idan an yi ruwa, duk da dai mun san ana kokari musamman kantoman riko na karamar hukumar Jama’a, Mista Katuka Bege, wanda ya ziyarci kasuwan da kansa ya duba irin gyare-gyaren da take bukata kuma har ma wasu kamfanoni sun zo sun duba,” inji shi.
A karshe shugaban ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su hada kai, musamman wadanda suka fadi takara a zaben da ya gudana kwanan nan.
A farkon watan Mayu ne aka gudanar da zaben shugabannin babbar kasuwar Kafanchan.