✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace gwamnati ta sake fasalin takardun kudinmu?

A makon jiya ne aka shiga yada jita-jitar cewa an daina karbar takardun kudi masu liki ko wadannda suka yage ko suka tsufa, hakan ya…

A makon jiya ne aka shiga yada jita-jitar cewa an daina karbar takardun kudi masu liki ko wadannda suka yage ko suka tsufa, hakan ya jefa jama’a da dama cikin damuwa, duk da Babban Bankin Najeriya ya musanta zancen hana karbar takardun kudin da suka yage. Aminiya ta tuntubi jama’a a kan ko ya dace a sake fasalin takardun kudin kasar nan ganin cewa na yanzu musamman kananan suna saurin lalacewa:

 

Ya kamata a sauya –Aliyu Abdurrahaman ABU FM

Daga Aliyu Babankarfi Zariya

Ni a ra’ayina ya kamata a sauya fasalin kudin Najeriya ta yadda ba za su rika lalacewa da sauri ba, domin ’yan Najeriya muna da dabi’ar yi wa kudi rikon sakainar kashi ma’ana wadansunmu suna wulakanta takardun kudi, hakan ya sa suke saurin lalacewa. Don haka ina goyon bayan sauya fasalin takardun kudin Najeriya.

 

Bai dace ba –Sani Muhammad KT one T

Daga Aliyu Babankarfi, Zariya

A nawa ra’ayin bai dace ba saboda an dade ana sakewa amma babu wani sauyi da hakan ya kawo. Kawai gwamnatin ta maida hankali wurin dawo da darajarsu ta hanyar bude kamfanoni da samar da ayyukan yi ga al’umma ta hanyar kara karfin wutar lantarki a kasa.

 

Sakewar yana da kyau –Abdullahi Tukur

Daga Amina Abdullahi, Yola

Yana da kyau mu ga takardun kudinmu suna da kyau. Idan an lura za a ga yadda ake wulakanta takardun kudi a kasar nan. Wadansu sai su sa  a cikin manja, wani ya rubuta sunansa har da lambar waya a jikin takardar kudi. Wadda idan aka ba ka sai ka ga kai kanka bai kamata a yi hakan ba. Amma idan aka kwashe wadannan takardun kudi aka maida su banki, aka bugu sababbi hakan zai fi. Ina son a rika wayar wa al’umma kan wajen kula da takardun kudinmu. Ko ba komai tsabta na cikon addini ne. saboda haka a ra’ayina, a fitar da sababbin kudi a kwashe tsofaffin.

 

A fadakar da mutane muhimmancin kula da takardun kudin –Faruk Buba Wudil

Daga Muhammad Aminu Ahmad

To batun sake fasalin takardun kudinmu, ai a baya an sake fasalin kudin babu wani abu da ya canja. Dabi’armu ta ’yan Najeriya ta rashin daraja takardun kudinmu, da wulakantar da su ne abar dubawa. Don haka maimakon a sake musu fasali gara a rika fadakar da mutane kan muhimmancin kula da takardun kudadenmu. Kuma gara a ci gaba da amfani da kudaden na leda maimakon sake wasu.

 

Zai iya karya tattalin arziki–Ado Garba Wudil

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiyar magana batun sake fasalin  takardun kudi, koma baya ne domin abu ne da zai iya kawo nakasu ga ci gaban tattalin arzikin kasa. Ba don komai ba sai irin kudaden da za a kashe wajen sake fasalin kudin shi ma ya isa kasar nan ta yi wani abu na amfanin al’umma. Don haka maimakon yin wannan gara matattun kudaden a janye su daga hannun jama’a a sake buga su, don su maye wadancan da aka janye.

 

Ba na goyon baya – Padia Phineas

Daga Amina Abdullahi, Yola

Wani lokaci mutum yana iya cewa eh ko aa. Amma kawo yanzu zan iya cewa na tsaya a kan a’a. Domin an sha canja takardun kudi a kasar nan kuma a dan karamin fahimtar da muke da shi, duk sa’ar da aka canja kudin, ba karamin kudi ake kashewa ba kafin a yi sababbin takardun kudin, a gabatar wa gwamnati ta amince da su sannan a buga su. Sannan abin da ake ciki duk shi ne ba a kasar nan ake buga kudaden nan ba. Kasashen waje ake ba kwangilar wannan aiki kuma da makudan kudi.