Shugaban Kwamitin koli na kungiyoyin Aikin Gayya ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Garba Aminu kofar Na’isa ya ce idan aka farfado da kungiyoyin aikin gayya za a kara samun nasarori wajen kawar da duk wata shara da ke Birnin Kano da kewaye.
Shugaban ya yi bayanin ne yayin da yake duba wani aikin gayya da aka gudanar a Birnin Kano, inda ya ce gwamnatin Jihar Kano ta dauki tsaftar muhalli da matukar muhimmanci don haka yana da kyau kungiyoyin aikin gayya su kara himma wajen tabbatar da ganin ana samun cikakkiyar tsaftar muhalli.
Ya kara da cewa: “Idan aka farfado da ayyukan kungiyoyin aikin gayya da ke fadin jihar, ko shakka babu za a kara zage damtse wajen tsaftace birni da yankunan karkara kamar yadda ake haduwa ayi a lokutan baya.”
Daga nan ya ce bayan aikin shara suna gudanar da aikace-aikace na kwashe shara da yashe magudanun ruwa a wasu sassa na Birnin Kano, sai dai a cewarsa yana da kyau gwamnatin jihar ta samar da kayan aiki ga kungiyoyin aikin gayya da ke fadin jihar ta yadda za su kara himma wajen inganta yanayin muhalli da bunkasa tsafta.
A karshe shugaban ya yaba wa hukumar kwashe shara ta jihar saboda bullo da aikin kwashe shara, wanda hakan a cewarsa zai taimaka wajen tabbatar da tsaftace tituna da kasuwanni da kuma tashoshin mota. Har ila yau, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya a kokarin ta na inganta yanayin muhalli a fadin jihar.