An gurfanar da wani mutum mai suna Abdullahi Idris, a gaban kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano, saboda zargin ƙone budurwarsa, Sa’adatu Ibrahim, saboda ta ƙi amincewa da aurensa.
Idris, wanda yake zaune a garin Rimi, ƙaramar hukumar Sumaila, ya kasance yana soyayya da Sa’adatu, wadda bazawara ce.
- DAGA LARABA: Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Idan Tana Son Hana Zanga-Zanga
- EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON kan aikin Hajjin 2024
Ya shafe tsawon kwanaki bakwai yana muradin ta amince da batun aurensa amma ta ƙi amincewa da buƙatar tayin da ya mata.
An tuhume shi da laifin yin sharri, ƙone mutum, da yunƙurin kisan kai, sai dai duk da haka ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa.
Lauyan mai shigar da ƙara, Barrista Maryam Jubril, ta nemi a ɗage shari’ar zuwa wani lokaci.