Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Bayer Leverkusen, wanda tsohon dan wasan kungiyar Real Madrid ne ake sa ran zai maye gurbin Kocin Real Madrid na yanzu, Carlo Ancelotti, wanda shi kuma ake sa ran zai koma horar da kasar Brazil.
Jaridar Radio MARCA ce ta ruwaito kungiyar ta amince ta dauki tsohon dan wasan nata, domin maye gurbin kocin na yanzu.
Alonso ya yi shekara shida a Real Madrid a matsayin dan wasa, sannan ya yi aikin horar da matasan ’yan wasan kungiyar.
Da yake jawabi game da yiwuwar maye gurbinsa a kakar badi, Carlo Ancelotti ya bayyana cewa Xabi zai iya aikin.
A cewarsa, “Ina da burin ganin Xabi Alonso ko Raul ko Alvaro Arbeloa waninsu ya zama kocin Real Madrid wata rana. Ina kaunarsu sosai.”
Sai ya kebe Xabi da cewa, “Ya fahimci harkar kwallo sosai. Na horar da shi a baya, kuma mutum ne mai kwarewa sosai.
“Kuma yanzu haka yana kokari sosai a kungiyar Bayer. Fahimtar da ya yi wa kwallo ne sosai ta sa yake kokari matuka a matsayinsa koci.”
A watan Oktoban bara ce Alonso ya zama kocin Kungiyar Bayer Leverkusen, inda kafin nan ya horar da matasan kungiyar Real Sociedad na shekara uku bayan horar da matasan Madrid da ya taba yi.
Amma a bangaren horar da manyan ’yan wasa, ko shekara daya bai yi ba, domin a bara ya fara, sai dai ana ganin ya fara da kafar dama.
A wani lokaci a baya, Jose Mourinho ya bayyana cewa yana da yakinin Xabi Alonso zai iya zama kwararren koci a duniyar kwallon kafa.
Mahaifin Alonso, Periko shi ma tsohon dan kwallo ne, inda ya lashe gasar La Liga guda uku, biyu a Real Sociedad, daya a Barcelona, sannan ya buga wa kasar Spain kwallo, inda ya kasance cikin ’yan wasa kasar da suka buga gasar Kofin Duniya ta 1982.
Daga baya kuma ya zama koci shi ma, inda ya horar da kungiyoyi da dama, ciki har da Real Sociedad.
Kaninsa kuma, Mikel ya buga wa Real Sociedad, Bolton da Charlton, sannan yana da wani kani Jon wanda shi kuma rafari ne na kwallon kafa.
Bayan haka, shi da Kocin Arsenal na yanzu, Mikel Arteta, abokan juna ne tun suna kananan yara a unguwarsu ta Calle Matia a kasar Spain.
A kungiyoyin da ya buga, Alonso ya lashe gasar Zakarun Turai a Kungiyar Liverpool da Real Madrid, sannan ya lashe Kofin Bundesliga da Kofin Kalubale na Italiya da na Jamus da Spain da sauransu.
A wasan gida kuwa, ya lashe gasar Kofin Duniya a shekarar 2010, da gasar Nahiyar Turai ta shekarar 2008 da 2012.
Kocin ya jagoranci Kungiyar Bayer Leverkusen zuwa wasan kusa da karshe na Gasar Europa ta bara.
Wadanda suka horar da Alonso
Daga cikin wadanda Alonso ya yi aiki da su a matsayin masu horar da shi akwai Carlo Ancelotti da Pep Guardiola da Jose Mourinho da Manuel Pellegrini da Rafael Benitez da sauransu.