✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Xan jarida ya zama Shugaban kulob xin Warri Wolves

Tsohon xan jarida mai rubuta labarin wasanni a Jihar Delta Moses Etu ya zama sabon shugaban qungiyar qwallon qafa ta Warri Wolves.Bayanin haka na qunshe…

Tsohon xan jarida mai rubuta labarin wasanni a Jihar Delta Moses Etu ya zama sabon shugaban qungiyar qwallon qafa ta Warri Wolves.
Bayanin haka na qunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin Jihar Delta ta fitar jim kaxan bayan ta rushe hukumar gudanarwar kulob xin da ke qarqashin Davidson Uwumi inda ta maye gurbinsu da sababbi.
Mista Moses Etu a da shi ne jami’in hulxa da jama’a na qungiyar, a yanzu ya samu wannan xaukaka ce bayan da gwamnati ta nemi da ya yi amfani da basirarsa wajen xaukaka martabar kulob xin musamman a wannan lokaci da kulob xin zai fafata a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Afirka (CAF Champions League) wanda za a fara a watan gobe.
Haka kuma gwamnatin ta buqace shi da ya yi duk mai yiwuwa don ganin kulob xin ya lashe wani kofi a karon farko tun bayan da aka qirqiro kulob xin a shekarun baya.