✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ta sake daukewa a Najeriya gaba daya

Har yanzu ba a bayyana musabbabin daukewar wutar ba

A karo na hudu cikin shekarar nan, wutar lantarki ta sake dauke wa a Najeriya gaba daya, inda ilahirin injinan tunkudo wutar suka daina aiki.

Najeriya dai a bana na yawan fama da daukewar wuta, inda ko a ranar takwas ga watan Afrilun 2022 wutar ta dauke dungurum-gum.

A cewar wani babban jami’i a Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (GenCo), an sami matsalar ne wajen karfe 6:00 na yammacin Lahadi.

“Mun fuskanci tsayawar injinan samar da wutar lantarki da misalin karfe 6:49 na yammacin Lahadi,” inji jami’in.

Ya zuwa lokacin daukewar dai, kamfanin na samar da megawat 1,353.80 ne, wanda kamfanoni 13 suke samarwa kafin a sami matsalar.

Akwai dai akalla kamfanoni 24 da ke samar da wutar, amma ko daga cikin guda 13 da suke aiki, guda hudu ne kawai suke samar da wutar ta ku-zo-ku-gani.

Dukkan manyan injinan da ke samar da wutar daga tashoshin lantarki na Kainji da Shiroro da Jebba su ma sun tsaya.

Rahotanni daga Kamfanin Wutar Lantarki na Kasa (TCN) na nuna cewa an sami koma-baya matuka a bangaren samar da wutar a ’yan kwanakin nan.

Mafi yawan wutar da aka samar ranar Asabar ba ta wuce megawat 3,685 ba, kuma ita ce adadi mafi yawa na wutar da aka samar a cikin makon nan mai karewa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, TCN bai fitar da wata sanarwa kan musabbabin tsayawar injinan wutar ba.

Amma wani jami’i a kamfan ya ce suna nan suna aiki ba dare ba rana wajen dawo da wutar a Abuja da wasu Jihohin tukunna.