Wani rahoto kan kasashen da suka fi fama da matsalar wutar lantarki a duniya ya nuna cewa a Najeriya ana dauke wuta kusan sau 400 a shekara.
Rahoton da cibiyar Utility Bidder ta kasar Birtaniya ta fitar na nuni da cewa ana dauke wutar lantarki akalla sau 394 a duk shekara a Najeriya, wanda shi ne mafi muni a Afirka.
Hakan na nufin adadin dauke wutar da ake yi a kasar a duk shekara ya haura yawan kwanakin shekarar.
Cibiyar Utility Bidder wadda ke bincike kan dauke wutar lantarki da kuma asarar da hakan ke haifarwa a bangaren masana’antu ta bayyana cewa kasa ta biyu wajen dauke wuta a Afirka ita ce Afirka ta Tsakiya (CAR), amma na Najeriya ya zarce nata sau 46.
Ga dai jerin kasashen Afirka 10 da aka fi dauke wuta a Afirka da kuma adadin dauke wutarsu a shekara:
- Najeriya – 394
- Afirka ta tsakiya – 349
- Benin – 336
- Nijar – 264
- Congo – 258
- Gambia – 253
- Burundi – 199
- Zambia – 160
- DR Congo – 148
- Burkina Faso – 118
Rashin tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya ya zame mata abin gori daga makwabtanta, musamman lokacin Gasar Kofin Nahitar Afirka (AFCON).
Aminiya ta lura cewa kasashen Afirka shida na daga cikin jerin kasashe 10 da matsalar ta fi kamari a duniya.
Kasashe 10 mafiya matsalar lantarki duniya:
- Papua New Guinea – 503
- Yemen – 466
- Najeriya – 394
- Afirka ta tsakiya – 349
- Benin – 336
- Bangladesh – 314
- Pakistan – 264
- Nijar – 264
- Congo – 258
- Gambia – 253
Rahoton ya nuna masana’antun CAR sun fi tafka asara da kashi 25% na kayan da suke samarwa a sakamakon dauke wutar a kasar, wanda shi ne mafi muni a duniya.
Afirka ce nahiyar da ta fi tafka asara bisa wannan dalilin da kashi 7.8% na abubuwan da take samarwa.
Mai bi mata ita ce Asia da kashi 4% na Asia, sai kasashen Latin kashi 2.2%, sannan turai kashi 0.7%.