✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar Lantarki: Minista ya ba da umarnin dawo da wutar Kano

An kara wa kamfanoni wa'adin kwana 60 su biya bashi

Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, ya ba da umarnin a dawo da wutar da aka yanke wa Kamfanin Wutar Lanarki na Kano (KAEDCO) saboda taurin bashi.

Ministan ya umarci Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya dawo wa KAEDCO da kuma kamfanin Kaduna Electric da kuma na Abba (APLE) wutar ne daga karfe 12 na daren yau Litinin 1 ga watan Mayu, 2023.

Sanarwar da Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Kasa ta fitar ta ce, za a dawo wa kamfanonin da wutar ne bayan ministan ya sanya baki, da nufin rage wahalar da rashin wutar ta jefa masu amfani da ita.

Ministan ya bukaci TCN ya kara wa kamfanonin da ma sauran wadanda yake bi bashi kwana 60 domin su samu su biya.

“Idan wa’adin ya cika, kamfanin zai katse duk masu taurin bashin, don haka ya kamata su yi amfani da kwana 60 da aka bayar wajen sauke nauyi da cika alkawarin,” in ji sanawar.

A kwanakin baya ne TCN ya yanke wasu layukan da yake ba wa kamfanonin wutar lantarki, saboda rashin biyan bashin da yake bin su na biliyoyin Naira.

A kan haka ne kamfanin ya katse wutar da yake bayarwa a wasu layukan da kamfanonin ke amfani da su wajen rarraba wutar lantarki.

Matakin kamfanin ya jefa yankuna da dama cikin duhu, lamarin da ya sa a wasu lokutan kamfanonin suka koma yin karba-karba wajen bayar da wutar.

Ko a ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito TCN na cewa yanke wutar da ta yi wa KAEDCO mai rarraba wutar lantarki a jihohin Kano da Jigawa da Kebbi, somin-tabi ne.

Amma KAEDCO ta ce tana tattaunawa da kamfanin da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an shawo kan matsalar.

A Kaduna, kamfanin Kaduna Electric ya dora laifin karancin wutar lantarki a jihar a kan rashin samun wutar daga TCN, wanda ya alakanta da rashin biyan kudin wuta da mutane ke yi.