Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya musanta kai karar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kotu.
BBC ya ruwaito gwamnan yana bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani taro da manyan jam’iyyar a birnin Fatakwal.
Gwamna Wike ya kuma ce bai bai wa kowa izinin kai kararsu kotu ba.
Tun da fari, wasu jaridun kasar sun rawaito cewa Wike da wani kusa a PDP mai suna Newgent Ekamon sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/782/2022 da ke kalubalantar janyewar Tambuwal daga zaben fitar da gwani da kuma goyon bayan Atiku.
A sammacin da Aminiya ta ruwaito, an sanya PDP a matsayin wanda ake kara ta farko, sai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a matsayi wadda ake kara ta biyu, Tambuwal da Atiku a matsayin na uku da na hudu.
Daga cikin batutuwan da aka lissafo, Wike da Ekamon sun nemi kotun da ta umarci INEC da ta hana Atiku takara a zaben shugaban kasa na 2023.
Tuni aka fara rade-radin cewa Gwamna Wike na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.
Wasu rahotanni sun ce an cire tutocin ofishin Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, lamarin da ya haifar da yamutsi aka shiga tunanin ko maganar shirye-shiryen ficewar Wike daga PDP na dab da faruwa.