Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya isa birnin Fatakwal a bisa gayyatar Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, don kaddamar da wasu ayyukan raya kasa a jihar.
Kwankwaso shi da ‘yan rakiyarsa sun sauka Fatakwal ne da safiyar Litinin inda suka wuce kai tsaye zuwa gidan Gwamna Wike na kashin kansa da ke Rumuperikom, a karamar hukumar Abio Akpor, inda Gwamnan ya tarbe su.
- Sarkin Musulmi ya ziyarci Wike a Fatakwal
- HOTUNA: Sarkin Kano ya bude cibiyar kula da masu cutar kansa a Ribas
Wike ya gayyaci Kwankwaso, wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano ne domin ya kaddamar da sabbin titunan cikin garin Mgbutanwo da ke Karamar Hukumar Emohua ta jihar.
Kwankwaso shi ne dan siyasa na biyu daga wata jam’iyya da Wike ya gayyato domin kaddamar da aikin raya kasa da gwamnatinsa ta yi.
A baya, ya gayyaci Peter Obi na jam’iyyr LP, wanda ya hakan ya janyo cece-ku ce a jam’iyyarsa ta PDP wacce yake rigima da dan takararta na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.
A makon da ya gabata kuma Gwamnan ya gayyaci Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, inda ya kaddamar da Cibiyar Kula da Masu Cutar Kansa da Ciwon Zuciya ta Peter Odili da ke Fatakwal.