Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na wucin-gadi a Jam’iyyar APC Ibrahim Masari, ya ce Gwannan Jihar Ribas, Nyesom Wike, babban dan siyasa ne da zai taimaka wa nasarar dan takarar shugaban kasar jam’iyarsu Bola Tinubu a zaben 2023.
Masari ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, inda ya ce Wike ya cancanci rike kujerar mataimakin shugaban kasa a jam’iyar.
- A Yammacin Alhamis za a raba jadawalin Gasar Zakarun Turai na 2022/23
- Budurwar fitaccen mai gabatar da shiri za ta haifi dansa na 10
Masari ya kuma gaskata cewa an yi taro a Landan tsakanin Wike da Tinubu, kan yadda za su hada hannu da shi a APC a zaben 2023.
“Dalili kuwa shi ne Wike babban dan siyasa ne, kuma gwamnan ne da ke da karfin iko ba a jiharsa kadai ba, har da wasu da dama.
“Mutumin kirki ne mai kuma mu’amala da muatnen kirki; Muna fata zai taimaka mana samun nasara a 2023”, in ji Masari.
Ya ci gaba da cewa, “Idan za ka iya tunawa, wasu ’ya’yan jam’iyarmu ta APC ne suka ba da gudummawa wajen kada ita a zaben Jihar Bauchi da Adamawa, don haka ba sai mutum ya baro jami’yarsa zai taya ka cin zabe ba.
“Sannan kuma muna alfahari da yadda dan takararmu, Bola Ahmed Tinubu, ya karbu a wurin ’yan Najeriya.
“Don haka ko shakka ba na yi, za mu samu nasara a zaben 2023, ko da taimakon wani ko babu,” in ji shi.