✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wike ya ba wa ma’aikata hutu domin tarbar Tinubu a Ribas

Wike ya ce abin alfaharin Jihar Ribas da zababben shugaban kasa Tinubu zai kai ziyarar aikinsa ta farko bayan cin zabe

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu domin tarbar zaben shugaban kasa, Bola Tinudu a ziyarar da zai kai jihar.

Wike, wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne da ke takun saka da dan takarar shguaban kasa na jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, ya ce yayin ziyarar aikin ta kwana biyu, Tinubu zai kaddamar da gadar sama da ginin zamani da ya gina wa kottun Majistare a birnin Fatakwal, hedikwatar jihar.

Wike wanda ya juya wa Atiku baya a zaben da Tinubu ya lashe, ya ce, “Ina kira ga daukacin al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwato su yi wa zabebban shugaban kasarmu kuma abin alfaharimu, Mai Girma Sanata Bola Ahmed Tinubu gagarumar tarba, tare da bayyana abin da aka san su da shi na karamci yayin a ziyarar da zai kaddamar da muhimman ayyukan ci gaba da za su zama tarihi.

“Saboda haka na ayyana ranar Laraba, 3 ga Mayu 2023, a matsayin ranar hutu domin muane su samu damar fita su yi wa zababben shugaban kasa maraba.

“Hakazalika daga karfe 8 na safe zuwa 3 na yinin ranar shaguna da wuraren kasuwanci da ke kan titin Rumuola zuwa Rumuokwuta a Karamar Hukumar Obio/Akpor za su kasance a rufe.

“Saboda haka ina kira ga kungiyoyin kwadago da hukumomin tsaro su ba da hadin kai su kuma tabbatar da wannan umarni,” in ji Gwamnan Wike, a jawabinsa ga jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa tun a lokacin ziyarar Tinubu na yakin neman zabe a jihar, ya nuna sha’awarsa ta gayyatar sa domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar.

Bayan kammaala zaben kuma ya aika wa zababben shugaban kasan goron gayyata, kuma ya amsa cewa a jihar zai fara  kai ziyarar aikinsa ta farko bayan zabe.

Wike ya ce, “Abin alfaharin gwamnatinmu ne ziyarar da zababben shugaban kasa zai kawo wannan ziyara mai tarihi ga al’ummar Jihar Ribas.”