Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayar da gudunmawar motocin bas-bas guda 25 domin tallafa wa yakin neman zaben jam’iyyar PDP na 2023 a jihar Binuwai.
Gwamnan jihar ta Binuwai, Samuel Ortom, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin kaddamar da tsarin yakin neman zaben jam’iyyar na jihar da kuma kwamitin gudanar da yakin neman zabenta.
- Zargin sakin tsohon Kwamishinan da ya ‘kashe’ abokinsa ya jawo zanga-zanga a Bauchi
- Za mu kawo karshen matsalar tsaro a wata 6 in muka ci zabe – Kashim Shettima
Ya ce Gwamnan na Ribas, wanda abokinsa ne ya bayar da sabbin motoci kirar Hiace guda 25 ga kwamitin yakin neman jam’iyyar domin saukaka zirga-zirga a lokacin tarukan siyasa.
“Kowace Karamar Hukuma da ke jihar za ta samu motar bas daya, Wike ya kuma yi alkawarin halartar taron gangamin yakin neman zabe a jihar a ranar Litinin mai zuwa,” inji shi.
Ortom ya kuma yaba wa Gwamna Wike kan yadda ya kasance tare da mutanen Binuwai a duk lokacin da suke da bukatar wani abu.
Gwamnan na Binuwai ya kuma ce da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fito fili ya tunkari kalubalen da ke dabaibaye jam’iyyar, za su yi aiki tare don ceto Najeriya, inda ya ce ba shi da wata matsala da kowa.
“Abin da ni da takwarorina ke bukata shi ne kwamitin ya magance matsalolin da suka shafi kowa da kowa. Idan ba a warware batutuwan da Gwamnoni biyar muka gabatar ba, ba zan bayar da tabbacin da abin da zai faru a zaben Shugaban Kasa ba,” inji Ortom.
Tun da farko, Mukaddashin Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Isaac Mffo, ya bayar da tabbacin jam’iyyar za ta sami gagarumar nasara a zaben 2023, inda ya jaddada cewa jam’iyyar ba ta da abokin adawa a jihar.