Gwamnatin Jihar Ribas, ta karfafa haramcin da ta sanya a kan ayyukan kungiyar ’yan awaren Biafra (IPOB), kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta yi umarnin daukar kungiyar a matsayin haramtacciya.
Gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya yi shelar neman wani jagoran kungiyar Stanley Mgbere ruwa a jallo, inda ya bayyana wata gagarumar kyauta ga duk wanda ya yi katarin isar da cikakken bayanan inda za a same shi a ko ina yake.
- Gwamnatin Filato ta sake dawo da dokar hana fita
- Yadda kalaman Nnamdi Kanu suka fusata tsofaffin Shugabannin Najeriya
Wike ya ce a shirye yake ya ba da tukwicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya shigar da bayanan da suka yi tasiri wajen samun nasarar gano inda jagoran kungiyar ta IPOB yake da kuma cafke shi.
Gwamna Wike ya sanar da hakan ne a jawaban da ya gabatar a daren Juma’a, inda ya ce daga yanzu ba za a lamunci kowace kungiya ta fito tattaki na tayar da kayar baya ba a jiharsa.
Furucin da Gwamnan ya yi yayin da ya bayyana Stanley Mgbere, a matsayin mutumin da ake nema ruwa a jallo, sakamakon jagorantar mambobin kungiyar IPOB wajen tayar da tarzoma da ta salwantar da rayuka da dukiyar al’umma a Karamar Hukuma Oyigbo ta jihar.
Bayanin haka na kunshe cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun Gwamnan, Kelvin Ebiri ya ambata wa manema labarai a daren Juma’a.