✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WHO ta soma aikin saukaka samar da rigakafin Kyandar Biri

Hukumar ta nuna damuwa kan yadda cutar ke ci gaba da yaduwa

A kokarin da take yi na yaki da cutar Kyandar Biri, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, ta soma aikin saukaka hanyoyin samun rigakafin cutar duba da yadda bukatar ta ke karuwa a sassan duniya.

Babban Daraktan hukumar, Dokta Tedros Ghebreyesus ne ya  bayyana haka ranar Talata a wajen babban taron da aka gudanar a Geneva.

Ghebreyesus ya ce, WHO ta fitar da ka’idoji dangane da cutar kyandar biri da kuma shawarwari ga gwamnatoci dangane da yaki da cutar.

Da yake zantawa da manema labarai a wajen taron, kwararre a hukumar, Dokta Rosamund Lewis, ya ce abu ne mai matukar muhimmanci wayar wa al’umma kai dangane da irin hadarin da ke tattare da cutar hanyoyin kariya daga barin kamuwa da cutar.

Masanin ya ce ana iya kamuwa da cutar kyandar biri idan aka yi mu’amala da wanda ke dauke da ita, don haka suka ce akwai bukatar yin kaffa-kaffa da duk wanda aka tabatara yana dauke dan ita.

Haka nan, ya ce tarayya wajen amfani da abubuwa kamar sutura, shimfida, kwano ko cokali da sauransu tare da mai dauke da cutar, ka iya zama hanyar kamuwa da cutar.

(NAN)