A tsakanin 11 zuwwa 13 ga Oktoba, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gudanar da shirin horarwa ga ’yan jarida fiye da 30 a Maiduguri kan yadda ake rahoton matakin gaggawar kula da lafiya. Wadanda suka samu horon an zabo su ne daga Jihohin Adamawa da Barno da Yobe. A cewar Dokta Chima Omuekwe, kwararren masanin sadarwa na Hukumar ta WHO, shirin an tsara shi ne don a nuna wa ’yan jarida managartan dabarun tsara rahotanni, ta yadda za a ceto rayuka a lokacin aukuwar bala’I da ke bukatar kulawar gaugawa, sannan a samar da kafa ga hukumar don hulda da ’yan jaridar da ke daukar rahotannin matsalolin kula da lafiya wajen kawo daukin gaggawa a yankin Arewa maso Gabas. Ya yi nuni da cewa kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen fadakar da al’umma kan yaduwar cututtuka da yadda za a shawo kansu, tare da nuna wa al’umma yadda za su sauya dabi’u zuwa managarta. “Kula da lafiyar al’umma kan yadda za a shawo kan cututtuka lokacin da ake bukatar daukin gaggawa, mutane sun fi kula da yadda za su kare kansu da iyalansu.
Rahotannin kafafen yada labarai, don haka ya kamata su dogara ne kacokan kan bayanan da za su taimaka wajen ceton rayuka,” inji shi.
Alhaji Haruna Baba-Sheikh Shugaban kungiyar ’yan jarida (NUJ) na Jihar Barno ya yaba kan wannan karamci, inda ya yi nuni da cewa za su yi kokarin fadada rahotannin kan al’amuran da suka shafi kula da lafiya a yankin.