Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bai wa Rundunar ’Yan Sandan Kano, kyautar babura guda 1,000.
Taron bayar da tallafin ya gudana ne a ranar Asabar a hedikwatar ’yan sandan da ke Bompai a Kano.
- An tsare shi kan zargin yin luwaɗi da yaran maƙocinsa 5 a Zariya
- Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabon Babban Hafsan Sojin Ƙasa
Ya bayar da tallafin ne domin taimaka wa jami’an ’yan sanda, wajen inganta ayyukansu da kuma tabbatar da tsaro a jihar.
Baburan waɗanda sabbi ne, kuma an ƙera su don yin aiki a kowane irin yanayi.
A shekarar 2023, Barau ya bai wa rundunar motocin aiki guda 22 domin tallafa wa ayyukanta.