Wani matashi mai shekaru 29, ya gurfana a gaban wata Kotun Majistare da ke Kaduna kan zargin sa da satar tsabar kudi har dubu 50 da kuma waya salula samfurin Infinix wacce darajarta ta kai Naira dubu 150.
Matashin wanda mazaunin layin Constitution ne a garin Kaduna, ana zarginsa da aikata laifuka biyu da suka hada da sata da kuma hadin baki.
- Za a dawo wa da Najeriya £4.2m da James Ibori ya boye a Birtaniya
- Mata sun yi gangamin yakar kashe-kashe a Zangon Kataf
Jami’in dan sanda mai shigar da kara Sufeta Chidi Leo, ya shaida wa Kotun cewa, wata mata mai suna Rakiya Theophilus ce ta shigar da korafinta kan lamarin a ofishin ’yan sanda da ke Gabasawa a ranar 2, ga watan Maris.
Leo ya ce a ranar ce da misalin karfe 3.45, wanda ake tuhumar tare da wasu mutane biyu suka shiga cikin shagon Rakiya da ke layin Kigo da zuwan za su saye wanduna.
Dan sandan ya ce, sai kuwa matashin da abokansa suka faki idanunta da yarinyar shagon a daidai lokacin da suke saurarar wasu abokanan cinikayyarsu da suka zo sayayya, suka dauke wayar salula samfurin Infinix sannan suka bude jakarta ta hannu suka debi kudi.
Leo ya ce laifin da ake tuhumar matasan ya saba da sashe na 234 da 245 na kundin dokokin miyagun laifuka na Jihar Kaduna.
Sai dai matashin ya musanta aikata laifin, yana mai cewa sam ba shi ba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.
Mai shari’a Ibrahim Emmanuel, ya bayar da belin wanda ake tuhumar kan kudi Naira dubu 100 sannan ya dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2021.