Shigowar wayar hannu wadda ake kira salula ta taimaka kwarai wajen saukaka harkar sadarwa a fadin duniyar nan tare da saukaka al’amura da dama na rayuwar yau da kullum.
Kafin shigowar wayar hannu ta tafi-da-gidanka ana amfani ne da waya mai amfani da wayoyin sadarwa wadanda ba a yawo da su sai dai a ajiye su a kan tebur a gida ko a ofis. Kwatsam sai Allah Ya kawo wani ci gaba a wannan fannin inda aka samu wayar da za a rika rikewa a hannu ana tafiya da ita ko’ina.
Da farkon fitowar wayar salula mallakarta sai wane da wane, amma da tafiya ta yi tafiya sai ga shi wayar ta zama gidan kowa da akwaita, tun daga Shugaban Kasa zuwa gyartai, maza da mata, babba da yaro kowa ya mallaki wayar hannu, ta yadda za a iya cewa, wadanda suka mallaki wayar har sun rinjayi marasa waya ko kuma a ce ana kankankan.
Babu shakka fitowar wayar ta haifar da alherai masu yawa da sharruka masu yawa, daga ciki akwai saukaka al’amura, domin ta taimaka wajen kara dankon zumunci ta yadda yanzu ’yan uwa da abokan arziki suna hulda da juna a kullum a duk inda suke a fadin duniyar nan. Yanzu ba ma magana da juna kawai ake yi ba, har ma ganin juna ake yi a yayin da ake maganar.
Sannan wayar nan ta taimaka wajen saukaka huldar kasuwanci, wanda ya sanya ake yin cinikayya ta waya ba tare an tashi an yi tafiya mai nisa ba, mutum zai iya sayen duk abin da yake so kuma a kawo masa har gida ta hanyar wayar salula. Haka ma harkokin banki duk waya ta saukaka su.
A sanadiyar wannan wayar yanzu tafiye-tafiye sun ragu sosai, domin mafi yawan harkoki ana iya yin su ta waya ba sai an tashi an tafi wani wuri ba. Hatta karatu ma duk ana yin sa ta waya. Harkoki da yawa sun yi sauki saboda samuwar wayar salula.
A yayin da za iya cewa akwai alherai da yawa da wayar salula ta samar, haka kuma akwai matsaloli da yawa da wayar ta haifar da su, daga cikinsu akwai yada labaran karya da yada fasadi da kulla mu’amalar banza a tsakanin mutane da koyar da sharri da sauransu da yawa.
Hatta garkuwa da mutane da yanzu ta zama ruwan dare wayar salula ce ta tabbatar da ita, domin ta hanyar wayar ce, masu garkuwa da mutane suke ciniki da ’yan uwan wadanda aka kama domin a ba su kudin da suke bukata. Za a iya fahimtar haka idan aka yi la’akari da labarin wani dan jarida wanda aka yi garkuwa da shi kwanan nan, inda ya bayyana cewa a cikin wadanda aka kama su tare akwai wata mata, amma da yake ba ta da waya a lokacin da aka kama su, masu garkuwa da mutanen ba su samu damar tuntubar ’yan uwanta ba, saboda haka dole suka sake ta bayan ta kwashe kwanaki takwas a hannunsu, kuma ko kwabo ba ta bayar ba saboda babu hanyar saduwa da ’yan uwanta.
A nan za a iya cewa rashin waya ya yi wa wannan matar amfani, sai dai kuma a wani lokacin yana iya zama matsala, domin idan aka fada hannun wadansu mugayen kashe mutum za su yi, tunda babu yadda za su yi su samu kudi, za su ce gara su kashe mutum maimakon su sake shi haka nan kawai. Allah dai Ya kare mu.
Saboda a rage aikata miyagun laifuffuka ne ya sanya gwamnati ta tilasta wa kamfanonin sadarwa su rika yi wa duk wanda ya mallaki layin waya rajista yadda za a rika gane mai layin a duk lokacin da aka bukaci hakan. Amma masu garkuwa da mutanen sai suka gane haka, saboda haka idan sun kama mutum sai su kwace wayar da ke hannunsa su rika amfani da ita wajen tuntubar ’yan uwansa, don haka babu yadda za a iya gane su ta hanyar wayar ke nan.
Saboda haka lokaci ya yi da za a samar da wata na’urar da za ta iya gano daidai wurin da mutum yake a lokacin da ya buga waya, ta yadda ko masu garkuwa da mutane sun yi amfani da wayar wanda suka kama za a iya gane daidai wurin da suke.
Haka kuma wannan na’urar za ta taimaka wajen rage yin karya ta waya, domin wani lokacin idan aka kira mutum idan yana Kaduna ne a lokacin sai ya ce, yana Abuja ne. Wani ma bai san cewa wanda ya kira shi yana kallonsa ba, amma sai ya sheka masa karya.
A baya kafin bayyanar wayar salula ba a san garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ba, sai dai a yi fashi ko a kama mutum domin a yi tsafi da shi a rika samun kudi, amma yanzu wayar salula ta sanya mutum ya zama kudi, za a kama shi yana da ransa da lafiyarsa a nemi wasu makudan kudi, kuma dole ’yan uwansa su nemo kudi su ba masu garkuwa da shi idan ba haka ba a hallaka dan uwan nasu.
Muna fata Allah Ya sa a gano wata hanya da za ta rika ganowa cikin sauri mugayen mutanen da suke amfani da waya suna cutar da jama’a.