Majigin Haurobiyana
Na-mujiya baibaiye da yana
Harigidon ’yar tsana
Hargowa da kisissina
Bujimi ya tunkuyi karsana
Manya masu dagawa
Suna ta tsiwa
Wai suna tare da talakawa
Alhali su ne ’yan wawa
Masu juyin katantanwa
Haurobiyawa
A kada musu kararrawa
Domin sun yi yawa
Miyagu na kyakkewa
’Yan adawa a kungurmin dawa
Masu hargowa
sun karke da rawa
suna juyi da takun ranwa
wulwulawar fedar laulawa
Sun gaza daura damin dawa
Mai gonakin Ottawa
’Yan tsaki sun yi yawa
Suna kin dangi
Don jefa jama’a kangi
Baba ya ki tankawa
Sun yi kidansu
Sun taka rawarsu
Samandagarin samarin kusu
Jaba da gafiya an yi busu-busu
Taron shassha da sususu
Harbin kunama
Ya haifar da rashin makama
Haurobiyawa mu yi magama
Tsiyataku sun tsima
Tsaminsu ya zarta fura tsantsama
Mai dan boto
Akwai kanzon kuregen rahoto
Kun fi kurciya koto
Al’umma na gwagwiyar toto
In hatsi ya kare sai a ranto
Baban-gargada
Baba yai gada-gada
Burgar sukuwar danda
Juyin masa a tanda
Kwankwadar makwalwar randa
Wa ya lakume ribar tekun Pasha
Ya bar mu muna assha-assha
Shi kuwa washa-washa
Ba ya kunyar aikin assha
Ya maishe mu ’yan tasha
Baban-burin-huriyya
Mai duka yai maka kariya
Miyagu na kurda-kurdar tsiya
Gida guda na daurin tsintsiya
Harbin magabtasai hatsabibiya
Wasikun wurgiya
Wutsil-wutsil din wafciya
Wuntsila gudi-gudin karafkiya
Walankeluwar kiren-karya
Walkiyar waskiya
Halin-burtu
Sunkurun shirya kutu-kutu
Jerin tsiyataku
Sun yi wa kasa katutu
Ana ta surutu rututu
Sun kakaba tagiyar Malam Mantau
Jiki magayi shan tabar dan Korau
An ji jiki rau-rau
Ana gani da na-mujiya tarau
A kakaba tagiyar Malam Tunau
Miyagu na wasan majigi
kurungunsu na ta gigi
Wasunsu na magagi
Sun makale a sagagi
Shi ya sa suke ta kugi
Baba an yi taga-taga
Mun hango su ta taga
Suna hayagagar ayaga
dan akuya na ci maka danga
Mugu na taka rawar ganga
Ka ga karen farauta
Yana so a fafata
Har ya feke farata
Shi ya shiga jerin zarata
Amma fa mabarnata
Ana ta wasan kwailkwayo
Wannan ya kewayo
Wancan ya zagayo
Akuya ta tunkuyi kwikuyo
A majigin marasa wayo
Salon sunkuyo
Sukuwar sakatar Saliyo
Sakarkaru sun sulmiyo
Baragurbi sun bibiyo
Ambaliya aka antayo
Burgu
Yai muku dungu
Kai mugu
Sai an kama maka kugu
Har ka gaza juyin kidan kalangu
Tereren tsiyaku
Magabta sun ci cuku
Tuni sun dakku
Saura kamun matsattsaku
Ko damkar kazar kuku
Masu taron dangi
Manufarsu tarwatsa al’umma
Talakawa su yi ta hamma
A kasa batun kalma da kalama
Kowa yai ta jan dagi
Iro Mugun madambaci
Kuliya da kusu na son su ci
Ina tarkon kama macuci
berayen da suka yi butulci
Da kasurgumin mai nukuburci
Al’umma
Kowa ya kara himma
Wajen fardar garka da gayauna
Mu samu abin kai wa ma’auna
Aikin gama ya gama
Kowa sai ya dama
Kurda-kurda da dama-dama
Masu tsiya-tsiya na ta kyarma
An fi karfin masu karma-karma
Tsintsiyar Baba na ta kara kima
Nai horon sanin makama
Ba na aikin dan kama
kwazon aiki ke sani azama
Kowa ya shigo a kama
Babbar manufar shukar alkama
Haurobiyana
Hatsaniya
Da hayaniya
kulle-kullen jefa magana
Maganganun rugugin ganguna
Babanmu ya kasaita
Azzalumai sun nakalta
Wasunsu sun hankalta
Miyagu kuwasun balbalta
Kyakkyawar manufa ta tabbata