✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila Kocin Chelsea ya koma AC Milan

A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din AC Milan wanda ya taba lashe kofin Zakarun kulob na Turai har sai 7 a tarihi,…

A ranar Litinin da ta gabata ne kulob din AC Milan wanda ya taba lashe kofin Zakarun kulob na Turai har sai 7 a tarihi, ya bayar da sanarwar korar kocinsa Montella inda nan take ya maye gurbinsa da Ganero Gattuso tsohon dan kwallon kulob din a matsayin kocin wucin gadi.

Sai dai ya zuwa shekaranjiya Laraba rahotanni da ke fitowa daga Italiya sun nuna tuni kulob din Milan ya fara tattaunawa da wakilan kocin Chelsea na Ingila Antonio Conte don mayar da shi kocinsu na dindindin.

daukar wannan mataki ya biyo bayan yadda kulob din ya samu nasara ne a wasanni biyu kacal daga wasanni 9 da ya buga a gasar rukunin Serie A ta Italiya a bana da hakan ta sa yake kasan tebur. 

Ganin yadda kulob din ya ware zunzurutun kudi har kimanin Fam Miliyan 150 a bara wajen cefano ’yan kwallo gami da rashin tabuka abin a zo a gani a kakar wasa ta bana, ya sa mahukunta kulob din daukar wannan mataki.

Kocin Chelsea da shi ma yake fuskantar matsala a Ingila, akwai yiwuwar ya amince da tayin da AC Milan ta yi masa don ya koma asalin kasarsa Italiya don ci gaba da horarwa a can.

Ya zuwa yanzu duniya ta zuba ido ne ta ga yadda al’amarin zai kaya, inda wasu ke ganin kocin zai tafi yayin da wasu ke hasashen da zuya kocin ya canza sheka a wannan lokaci.