✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watakila a dage gasar cin kofin Afirka na badi

Ganin yadda ake samun yaduwar cutar Ebola a kasashen Afirka, alamu sun nuna da wuya a yi gasar cin kofin Afirka a badi. Alamu sun…

Ganin yadda ake samun yaduwar cutar Ebola a kasashen Afirka, alamu sun nuna da wuya a yi gasar cin kofin Afirka a badi.

Alamu sun nuna haka ne tun bayan da Hukumar CAF ta kwace gasar daga Maroko kuma aka kasa samun kasar da ta nuna sha’awar daukar nauyin gasar saboda tsoron yaduwar cutar Ebola.
Mafi yawan kasashe suna son daukar nauyin gasar amma ganin yadda Ebola take yaduwa a Nahiyar Afirka ta sa da yawa daga cikinsu nokewa.
Sai dai ya zuwa wannan lokaci Hukumar ta ba ambaci kasar da za ta dauki nauyin gasar ba, amma dai ta bayar da umarnin a cigaba a fafatawa a kokarin ganin an fitar da kasashen da suka cancanci hayewa gasar. Hukumar ta tabbatar da cewa za ta ambaci kasar da za a yi gasar kafin a buga wasan karshe a ranar Laraba mai zuwa, idan kuwa ba haka ba, to ko shakka babu gasar ba za ta gudana a badi ba watakila sai a shekarar 2016.