✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata ta kona dan mijinta da miya

’Yan sanda a Jihar Kano sun kama wata mata  mai suna Hafsatu Sani da ke zaune a Unguwa Uku a birnin Kano bisa zarginta da…

’Yan sanda a Jihar Kano sun kama wata mata  mai suna Hafsatu Sani da ke zaune a Unguwa Uku a birnin Kano bisa zarginta da kona dan mijinta mai suna Ali Usman dan kimanin shekara 12 da tafasasshiyar miya lamarin da ya janyo dukkan jikinsa ya kone.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna  Abdullahi ya ce ana zargin matar ta aikata wannan aika-aika ne saboda yaron ya nemi asusunsa daga wurinta lamarin da ya fusata ta, ta dauko tukunyar miyar da ke tafasa a kan wuta ta sheka masa.

Yaron wanda mahaifiyarsa ba sa tare da mahaifinsa, ya shaida wa Aminiya cewa saboda gabatowar azumi da bikin Karamar Sallah ya sanya ya nemi matar mahaifinsa  ta ba shi asusun da yake tara kudi don yin wasu bukatu da suka shafi Sallah.

“Da ma ina dan tara kudina a asusun to yanzu sai na bukaci kudin don in sayi wani yadi da za a dinka min domin yin bikin Sallah saboda haka na nemi ta ba ni asusun. An dauki misalin kwana biyu ina tambayarta amma duk lokacin da na tambaye ta sai ta yi min fada, to a wannan lokaci da na tambaye ta sai ta dauko miya ta sheka min a jikina,” inji shi.