✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata Sabuwa: Sauya jaruma a shirin Alaka ya jayo ce-ce-ku-ce

Maryam Yahaya ta fito ne a shirin a matsayin shirinta na farko bayan doguwar jinya da ta yi

A zango na biyu na shirin Alaka mai dogon zango na Kamfanin FKD na Ali Nuhu, an yi mamakin ganin jaruma Maryam Yahaya.

Jarumar ta fito ne a shirin a matsayin shirinta na farko bayan doguwar jinya da ta yi.

Sai dai duk da cewa wasu na murnar ganin jarumar a shirin, wasu kuma tambaya suka fara yi kar dai a ce ita ce makwafin jaruma Habiba Y. Aliyu wadda ta fito a matsayin Ummi a shirin.

Ummi ta fito ne a matsayin kanwar Hisham da Nameer ’ya’yan Alhaji Alfindiki, inda take soyayya da wani talaka, amma yayanta, Hisham ba ya so har ya kore shi ya hana shi zuwa gidansu.

Duk da cewa jarumar sabuwa ce, ta ja hankalin masu kallon fim, inda wasu suka fara cewa ba za su ji dasi ba idan ta tabbata an cire ta, an maye gurbinta da Maryam Yahaya.

Fim din Alaka shi ne fim mai dogon zango na farko na Kamfanin FKD.

Dan Hajiya zai yi takarar dan majalisa

Fitaccen furodusan Kannywood, Naziru Auwal Dan Hajiya, ya sanar da cewa zai tsaya takarar Majalisar Jihar Kano a zave mai zuwa.

Dan Hajiya ya bayyana hakan ne a lokacin da ziyarci Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna.

Dan Hajiya ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “A jiya Talata na ziyarci Maigirma Maitamakin Gwamnan Kano Dokta Nasiru Yusuf Gawuna domin yi masa barka da shan ruwa, inda muka tattauna batutuwa na siyasa.

“Daga bisani na sanar da shi aniyata ta tsayawa takara ta Majalisar Jiha, inda ya yi farin ciki ya kuma ba ni shawarwari masu tarin yawa.”

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito a Wata Sabuwa cewa Lawal Ahmed shi ma zai tsaya takarar majalisar jiha a Katsina.

Tarbiyya: Jamilu Nafseen zai yi fim mai dogon zango

Marubucin Kannywood, Jamilu Nafseen zai tsara labarin wani fim da za a zagaya kasashe da yawa domin daukarsa.

Fim din mai suna Tarbiyya, an shirya zuwa kasashen Afirka da dama ne domin daukar fim din mai dogon zango.

Jamilu Nafseen dai marubuci ne matashi wanda a yanzu kuma ya fada harkar bayar da umarni a finafinai, musamman masu dogon zango.