✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata sabuwa: Cutar Ebola na sake barazana ga Najeriya

An gano masu sabuwar nau'in cutar COVID-19 mai saurin kisa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta gargadi ’yan Najeriya cewa bullar cutar Ebola a makwabtakan kasar na barazana gare ta, yayin da aka gano masu dauke da sabon nau’in cutar COVID-19 mai saurin kisa a kasar.

Shugaban Kwamitin Aiki da Cikawa kan Yaki da COVID-19 (PTF) kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce Najeriya za ta tsaurara matakan tantance lafiya a hanyoyin shiga kasarta musamman daga kasashen Guinea da Congo da aka samu bullar cutar Ebola.

“Za mu sa ido domin dakile yiwuwar yaki da cututtukan biyu a lokaci guda.

“Wannan nauyi ne ba a kan gwamnati kadai ba, daukacin ’yan Najeriya da sauran jama’a ma na da rawar da za su taka,” inji shi a lokacin jawabin Kwamitin a yammacin ranar Litinin a Abuja.

Sabon nau’in COVID-19 a Najeriya

A jawabinsa, Darakta-Janar na Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) Dokta Chikwe Ihekweazu, ya ce an gano mutum 29 da suka kamu da sabon nau’in cutar COVID-19 samfurin B.1.1.7 mai saurin kisa a jihohi daban-daban.

Ya ce domin samar da karin damar tuntubar NCDC, hukumar, ta samar da lambar kar-ta-kwana ta 6232 domin a kira a samu tabbatatttun bayanai game da cututtuka masu yaduwa.

Ya ce daga makon gobe PTF zai kaddamar ta tsarin tantance sakamakon gwajin cutar daga ko’ina a fadin duniya.

A nasa bangaren, Manajan kula da wadanda aka samu da cuta na PTF, Dokta Mukhtar Muhammad, ya ce Kwamitin zai sanya tsattsauran hukunci kan masu karya dokar kariyar cutar musamman masu shigowa daga kasashen waje.

Ya ce duk bakon da aka samu ya karya dokar to za a tsare shi a killace shi dole kuma shi zai biya kudin daga aljihunsa.

A Fabrairu za mu karbi rigakafin COVID-19 – Minista

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce kafin karshen watan Fabrairu Najeriya za ta karbi allurar rigakafin COVID-19 guda miliyan 16 a rukunin farko ta hannun kamfanin Vaccines Global Assess Facility.

Kasar ta kuma samu karin rigakafin guda 1.4 na kamfanin AstraZeneca daga cikin miliyan bakwai da kamfanin MTN ya ba ta gudunmuwa.

Ya bayyana cewa 500,000 daga cikin rigakafin na AstraZeneca za su iso kasar kafin karshen watan Fabrairu; ragowar 900,000 kuma zuwa karshen watan Maris, 2021.

Akalla mutun 1,750 ne cutar COVID-19 ta kasha a Najeriya tun bayan bullarta a wantan Fabrairun 2020.

Har zuwa bayan bullarta a karo na biyu a Najeriya, sama da mutumu 146,350 ne suka harbu da ita, kuma daga daga cikinsu fiye da mutun 121,190 sun warke, ta kuma yi ajalin akalla 35.