Tun kafin a kada gangar siyasar wasu sun yanke hukuncin duniya ta shiga uku, domin a fili yake cewa, Donald Trump ya hau hanyar lashe zaben Amurka a bana, inda giwa za ta take jaki! Akwai dalilai da dama da suka sa manazarta suka yanke hukuncin nasararsa.
Da farko Amurkawa mazauna gida sun fi jin dadi yadda yake barusa. Duk da yana da wuya a tarihin Amurka ku samu dan siyasa ya samu karbuwa a tashin farko na neman zama shugaban kasa, an saba farawa daga wani mataki kamar gwamna, dan majalisa ko sanata. Amma Donald ya kutsa kai!
Wannan dan takarar shagwababbe ne, kuma bai iya bakinsa ba. Bana zai cika shekaru 70 da haihuwa. Gani yake komai kudi ne, musamman ganin a wannan karon kudi sun yi tasiri. Shi bai taba wata sana’a ba ko aikin gwamnati sai neman kudi. A haka ake gani idan ya samu dama ba abin da zai yi sai mayar da mutane jari!
Ya yi suna wajen neman mata da sharholiya, inda ya auri sarauniyar kyau, kuma ya shahara wajen bunkasa kudin ruwa da tafiyar da gidajen caca. A haka ya yi wa kansa kirarin cewa, ba wanda ya kai shi nasarar a duk wadanda suka yi takarar shugaban kasa domin ya mayar da kwandala takarda! Ya mallaki biliyoyin daloli, amma hakan bai hana shi karbar bashi ba!
Manazarta da dama na ganin idan Donald Trump ya lashe zaben sai an gwammace kida da karatun, domin duk da zafin kan George Bush karami, wanda ya tsallake maganar majalisar wakilai ya kai hari Iraki tare da nuna sai ya sauya shugabanin kasashen da yake gani suna yi masa barzana, abin da ya haifar da rudu har wa yau a Gabas ta Tsakiya, gara shi.
Wannan mutumin zai iya sa ashana ya kyasta wa duniya wuta ko ya ba da umarnin da za a tada bom din nukliya don gwada tsagerancinsa. Kowa ya san Donald yana da zafin kai da takama kamar Hitila na Jamus.
Donald kan kira Amurka da sunan katafaren kamfani, inda ya nuna rayuwarsa na cikin da’ira, ko wace irin da’ira? Shi ya sani! An san yana daya daga cikin mutane 10 masu gidajen haya a Amurka, inda yake karbar kudin shaguna da gidaje ashawo da hanayen jari a kullum. A kuruciyarsa dan kwalisa ne, inda yake gabatar da wani wasan kwaikwayo mai taken ba da horo ga ‘yan nanaye. Ya taba shirya gasar sarauniyar kyau ta duniya, duk wadannan sun sa ya yi kaurin suna. Yayin da suke da muhimmanci a siyasar duniya.
Tun a zaben fida gwani ya yi wa abokin takararsa fintinkau a jam’iyyar Republican, inda ya kira Ted Cruz, ruwa biyu don ba a Amurka aka haife shi ba, haifaffen makwafciyar kasar ne, wato Kanada. Yayin da a jam’iyyar Democrat ake ganin uwar gida Hilary Clinton ta yi wa Bernie Sanders zarra da tserayya kadan. Duk da haka shugaba Obama ya ki ya fito fili ya mara wa dan takara daya baya a jam’iyyarsa, sai wanda ya lashe zaben.
Yayin da Obama ya nuna cewa Donald Trump ba zai iya rike Amurka ba.
Wani abu da ya sa ake ganin Donald Trump ya yi sa’a, shi ne, yadda kudi ke da tasiri, yayin da ba ya bukatar taimakon kowa. A lokacin da ake ganin ‘yan ta’adda da bakin haure ne manyan matsalolin dangantakar Amurka da kasashen ketare. Shi gani yake an wuce wurin!
Ganin abokiyar takararsa mace ce, duk da cewa, Hilary Clinton ta taka rawar gani a siyasar Amurka. Amma a halin yanzu an gaji da cika bakin da ‘yan jam’iyyar democrat suke yi na nuna kansu a matsayin masu kawo zaman lafiya da farfado da tattalin arziki. Domin Amurka ta tsaya cak, sai sallamar ma’aikata ake yi, kuma alakoa ta yi tsami tsakaninsu da sauran kasashen duniya.
A halin yanzu Mista Trump ya gaya wa Paparoma Magana, inda yake cewa, ‘idan Paparoma na bukatar tsaro to ya zabe shi.’ Ya tofa wa Paparoma miyau. To wa ya san abin da zai faru idan ya karbi ragamar kasar da ta fi kowace karfin soji da fada a ji a doron kasa?
Tabbas katange Musulmi daga Amurka ba zai bunkasa tattalin arzikin kasar ba. Sabanin yadda dan takarar yake nuna cewa, Musulmi da ‘yan unwasa Amurkawa na Kudu sun zama kaska a kasar. A yau duniya ta yi nisa an shiga zamanin gamuwa a yanar gizo ta yadda babu shamaki tsakanin jinsi balle jiha. Da kwamfutarka ko wayar selula za ka iya zakulo duk abin da kake bukata daga zaune a daki.
Wani abin takaici shi ne yadda Mista Trump yake da mashawarta da dubban masu ba da gudumuwa daga Yahudawa, inda Yahudu ke ganin za su kara samun gindin zama a Amurka da duniya baki daya idan nasu ya kai labari!
Kai abin Allah ya sawwake irin halin da duniya za ta fada domin wannan dan talikin. Daga hasumiyya zai koma White House, lallai za a ga sauyi daga attajirin da ya zama shugaban kasa. Maganar zahiri ba Musulmi kadai suke jin tsoron shugabancin Donald Trump ba, duniya za ta dandana!
Buhari Daure +2347035986444 Muryar Talaka kofar kaura, Katsina. [email protected].
Wata sabuwa a Amurka
Tun kafin a kada gangar siyasar wasu sun yanke hukuncin duniya ta shiga uku, domin a fili yake cewa, Donald Trump ya hau hanyar lashe…