An kama wata mata mai shekara 32 bisa zargin satar kwandon tumatir da tattasai a Jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne a Kasuwar Kulende da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu a ranar Laraba, bayan rahoton da ’yan kasuwar suka kai ga jami’an hukumar tsaro ta sibil difens.
- ’Yan bindiga sun sace basarake a Filato
- NAJERIYA A YAU: Ko Jam’iyyun Adawa Za Su Kwace Shugabancin Majalisa?
Tuni jami’an hukumar suka shiga tsakani don kwantar da tarzomar da ta tashi a kasuwar sakamakon kama matar.
Kakakin hukumar, Ayeni Olasunkanmi wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce wadda ake zargin ta saci “kwandon tumatir da na tattasai ta amsa laifin ta kuma za a dauki matakin shari’a a kanta nan ba da jimawa ba.”
An ruwaito cewar matsalar sace-sace a kasuwar ta zama ruwan dare tsakanin ’yan kasuwar.