✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta kashe kanta saboda nauyin bashi

Mutanen da ta karbi bashin a hannunsu ne suka yi mata matsin lambar biyansu kudinsu.

Gaza biyan bashi ya sa wata mata mai ’ya’ya hudu ta kashe kanta a unguwar Sobi da ke Karamar Hukumar Ilori ta Gabas a Jihar Kwara.

Matar mai shekaru 38, ta kashe kanta ne ta hanyar fadawa kogi sakamakon kasa biyan cikon dubu 30,000 daga 50,000 din da ta ranta domin bunkasa sana’arta.

Maigidanta da ba a bayyana sunansa ba, ya ce mutanen da ta karbi bashin a hannunsu ne suka yi mata matsin lambar biyansu kudinsu.

Ya ce gaza biyan bashin da mai dakin tasa ta yi ne ya sa suka shiga bata mata suna, lamarin da ya shigar da ita damuwa har ta kashe kanta.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Hassan Adekunle ya sanar da Aminiya cewa an gano gawar matar ne a kogin Awodi in da ta fada.