Jami’an Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP) sun cafke wata mata bisa zargin kashe jikarta ’yar shekara uku da duka.
Mai magana da yawun NAPTIP, Mista Anthony Okafor, ya ce sun kama wacce ake zargin ne bayan da hukumar makarantar da yarinyar ke zuwa ta kwarmata musu abin da ya faru ranar Alhamis a Awka, babban birnin Jihar Anambra.
- Yadda aka ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
- An gano gawa 13, mutum 10 sun bace a hatsarin kwalekwale a Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Yadda Abinci Ke Kashe ’Yan Najeriya
An damke matar ne a makarantar su yarinyar a daidai lokacin da ta yi kokarin karbar kudin makarantar da ta riga ta biya wa jikar tata.
Ya zuwa hada wannan labari, babu wani cikakken bayani kan dalilin da ya sa matar daukar wannan danyen hukunci kan jikar tata.
A cewar jami’in, “Da aka tambaye ta game da yarinyar, sai ta ce ta mutu. Ta ce yarinyar jikarta ce kuma shekarunta uku da haihuwa.
“Wacce ake zargin ta jagoranci jami’an NAPTIP zuwa inda ta boye gawar yarinyar.
“Ko da aka isa wurin, sai aka tarar ta nannade gawar cikin wata bakar jakar leda sannan ta jefar cikin ciyawa.
“An ce tun ranar 29 yarinyar ta mutu, kuma an mika matar ga ’yan sanda don ci gaba da bincike,” in ji shi.