Wata mata ’yar kasar Mali mai suna Halima Cissé mai shekara 25 ta haifi jarirai tara – lamarin da ya girgiza likitoci duk da irin binciken da suka gudanar kafin haihuwarta.
Halima, ta haifi jariran tara ne a kasar Maroko. Gwamnatin Mali ta dauki nauyinta domin samun kulawar kwararrun likitoci.
- ’Yan Hisbah sun kama mace da namiji suna lalata a tashar mota a Zamfara
- Zuwaira Ahmad: ‘Yar shekara 13 da ta rubuta Alqur’ani da ka
“Na yi farin ciki sosai,” kamar yadda mijinta ya shaida wa BBC.
“Matata da jariran da aka haifa (mata biyar da maza hudu) suna cikin koshin lafiya,” inji shi.
A shekarar 2009 wata ta haifi jarirai takwas a Amurka, kuma ita ce ke rike da kambun Kundin Tarihi na Duniya na wadda ta haifi jarirai mafiya yawa a lokaci guda, sannan suke cikin koshin lafiya.
A baya an taba samun wasu mata da suka haifi jarirai takwas a lokaci daya.
Wata ta haifi ’yan takwas a Ostireliya a 1971, sai wata mata a Malesiya da ta haifi ’yan takwas a 1999, amma babu daya daga cikin jariran da ya rayu bayan kwanaki da haihuwarsu.
Nadya Suleman, ita ce ke rike da kambun Tarihi na Duniya wajen haihuwar yara da yawa lokaci guda, yanzu haka yaran sun girma inda suka kai shekara 12 a duniya. Ministar Lafiya ta Mali, Fanta Siby ta taya ayarin likitoci a Mali da Maroko murnar yadda suka yi hidima har matar ta sauka lafiya.
Daraktan Kiwon Lafiya na Asibitin Ain Borja, Farfesa Youssef Alaoui da ke Kasabalanka, inda Misis Cissé ta haihu, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, ba kasafai ake samun mace ta haifi jarirai haka ba, inda ya ce abin ban-mamaki ne – kuma likitoci 10 da ma’aikatan lafiya 25 ne suka taimaka wajen haihuwar matar.
Nauyin jariran ya kai tsakanin giram 500 zuwa kilo daya, kuma ya ce za a ajiye su a cikin kwalbar kula da jarirai na tsawon wata biyu zuwa uku. Juna biyun Misis Cissé ya zama abin tsegumi a Mali duk da cewa gwajin da aka yi mata a farko-farko ya nuna jarirai bakwai take dauke da su, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana.
Likitoci a kasar da ke Afirka ta Arewa sun damu da yanayin kulawar da za ta samu bayan haihuwar jariran, hakan ne ya sa gwamnatin kasar ta kai mata dauki tare da fitar da ita zuwa kasar Maroko don ba ta kulawa ta musamman.
Bayan shafe mako biyu a wani asibiti a Bamako, babban birnin kasar Mali, an yanke shawarar mayar da Misis Cissé zuwa Maroko a wancan lokacin, kamar yadda Dokta Siby ta shaida wa Reuters.
Bayan shafe mako biyar a wani asibitin kasar Maroko, ta haihu a wani sashen kulawa na musamman a ranar Talata, in ji Ministar.
A cewar Farfesa Alaoui, Misis Cissé na dauke da juna biyu na mako 25 lokacin da aka kwantar da ita a asibitinsu kuma likitocinsu sun yi nasarar tsawaita wa’adin cikin zuwa mako 30.
Mijinta Kader Arby, ya ce “Allah ne Ya ba mu wadannan yara, Shi ne Ya san me zai same su, ban damu da abin da zai faru ba, idan Ubangiji Ya yi ikonSa, akwai dalili,” ya shaida wa BBC Afrikue.
Ya ce, ya ji dadin tallafin da iyalansa suka samu bayan haihuwar matar tasa.
“Kowa sai kirana yake yi! Kirana kawai ake yi! Hukumomin Mali sun kira ni a waya sun nuna farin cikinsu. Na gode musu… Shugaban kasa da kansa ma sai da ya kira ni ya min murna,” inji shi.