✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata cibiyar Musulunci a kasar Qatar ta karrama Sheikh Sani Rijiyar Lemo

An bayyana Tafsirin ‘Fayyataccen Bayani Na Ma’anoni da Shiriyar Alkur’ani’ na Sheikh Dokta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo a matsayin wanda ya lashe kyautar Sheikh…

An bayyana Tafsirin ‘Fayyataccen Bayani Na Ma’anoni da Shiriyar Alkur’ani’ na Sheikh Dokta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo a matsayin wanda ya lashe kyautar Sheikh Hamad ta 2020 da ake shirya wa a Kasar Qatar duk shekara.

A ranar Litinin cibiyar da ke daukar dawainiyar shirya gasar da ke fitar da fitatttun litittafan addinin Musulunci da aka wallafa a kowace shekara, ta bayyana tafsirin Shehin Malamin da aka wallafa cikin harshen Hausa a matsayin zakaran gwajin dafi na shekarar 2020.

Tunda farko cibiyar yada Addinin Musulunci ta kasar  Syria ce ta gabatar da sunan Shehin Malamain da Tafsirin nasa don neman a duba dace wa da cancantarsa kan bashi wannan kyauta bayan rahoton da Kwamitin kwararru daga kasashe daban-daban na duniya suka gabatar kan amincewa da bukatar karrama Malamin.

Littafin Tafsirin Alku’ani da Sheikh Umar Rijiyar Lemo ya wallafa.

Shehin Malami, Dokta Muhammad Sani Rijiyar Lemo, ya samu kasaitacciyar kyautar ta duniya bayan Sarkin kasar Qatar ya gayyace shi domin ya gabatar masa da ita bisa kokarinsa na karantar da Addinin Musulunci da harshen Hausa, musamman saboda wallafa babban tafsirin Alkur’ani na Hausa da ya yi wanda mutane da dama a duniya suka samu labarin kasaitaccen tafsirin na Hausa da babu tamkarsa tun gabanin fitowarsa kimanin makonni hudu da suka gaba, wanda yanzu haka ya karade kusan ko ina a ciki da wajen Najeriya.

Dokta Sani Rijiyar Lemo, Malami ne a Sashen koyar da Addinin Musulunci da Shari’a na Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma babban mai Da’awa da bayar da fatawa da karantar da Addinin Musulunci cikin harshen Hausa a Masallacin Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam na Usman Bn Affan da ke Kofar Gadon kaya a birnin Kano da ma sauran jihohi a Najeriya da kasashen Afirka.