Kimanin watanni biyar ke nan da fitaccen mawakin siyasar nan musamman wakokin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi kudade a hannun masoya Buhari domin yin sabuwar waka, amma har yanzu shiru.
A watan Satumban bara ne Rarara ya bukaci duk masoyi Buhari ya biya Naira dubu daya domin yin wata sabuwar waka, inda ya ce a wakar zai fito da ayyyukan da Shugaba Buhari ya yi, sannan ya nuna cewa shugaban yana da masoya.
- Sojoji sun hallaka kwamandojin Boko Haram 2 da ake nema ruwa a jallo a Borno
- ‘2023: Arewa za mu sake ba takarar Shugaban Kasa a PDP’
A cewarsa, wakar za ta kunshi ayyukan da shugaban ya yi guda 92 da zai yin bayaninsu a cikin a wakar domin nuna wa duniya cewa Buharin na aiki.
Ya kuma kara da cewa yana son masoya shugaban su tura kudin ne domin nuna cewa har yanzu yana da masoya savanin yadda wasu ke cewa masoyansa sun guje shi.
A wancan lokacin, Aminiya ta ruwaito a wani bayani ba ta iya tantancewa ba cewa cikin kankanin lokacin aka tara kudi sama da Naira miliyan 70, duk da cewa Aminiya ta tabbatar da wasu da suka tura kudin a wancan lokacin, inda wasu suke tura Naira dubu daya din, wasu suke tura sama da hakan.
Bukatar ta Rarara ta tayar da kura matuka a wancan lokacin, inda wasu mutane da dama suka rika fitowa fili suna kona kudadensu, tare da cewa gara su kona kudin da su bayar a yi wa Buhari waka.
Amma tun wancan lokacin, bayan kurar ta lafa, sai aka shiru daga mawakin.
Aminiya ta yi kokarin jin me ya sa har yanzu bai saki wakar ba bayan tabbatar da cewa ba a saki wakar ba, amma abin ya ci tura.
Sai dai ya zama abin wasa da dariya musamman a kafafen sada zumunta, inda wasu suke cewa ‘ya ci kudin’ ya ki sakin wakar.
A wani bangaren kuma, har yanzu ba a tabbatar da nawa mawakin ya tara ba, inda a nan ma wasu suke ganin ya kamata ya fito fili ya bayyana nawa aka tura masa.
Aminiya ta tuntubi wani mawakin wanda ba ya so a ambaci sunansa, wanda shi ma ya yi wa Shugaba Buhari wakar yakin neman zabe, inda ya ce, “a cewarsa, wai tana nan tafe. Amma ba abin mamaki ba ne idan ya ki yi duk da cewa ya amshi kudin mutane. Idan ba ka manta ba, an taba zargin cewa ya ci kudin mawaka da gwamnonin APC suka bayar.”
Rarara ya yi kyautar motoci
A kwanakin baya, mawakin ya ba da kyautar motoci ga wasu daga cikin ’yan fim, inda ya ba jaruma Jamila Nagudu da jarumi Tijjani Asase motoci.
Shi dai Rarara fitaccen mawaqin siyasa, inda a kwanakin bayan likkafarsa ta ci gaba, inda aka gan shi a kasar Nijar, inda ya rera wa dan takarar Shugaban Kasar Nijar Muhammadu Bazoum wakar yakin neman zabe.