✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata 1 bayan girgizar kasar da ta ci rayuka 50,000 a Turkiyya

’Yan kasar Turkiyya 45,968 da ’yan kasar Siriya 4,267 da ke gudun hijira a Turkiyya ne suka rasu a girgizar kasar

Wata guda ke nan bayan girgizar kasa da ta yi ajalin mutum sama da 50,000 a kasar Turkiyya.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce girgizar kasar ta ranar 6 ga watan Fabrairu, 2023 ita ce “iftila’i mafi muni” a cikin shekaru 100 da suka gabata a nahiyar Turai.

Wata daya ke nan bayan iftila’in, kuma hukumomin Turkiyya da makwabciyarta Siriya — wadda ita ma girgizar kasa ta shafa — suna fadi-tsahin aikin farfado da biranen da girgizar kasar ta yi lebur da su.

Dubban mutane ne dai suka rasu bayan gine-gine sun rufta a kansu, a yayin da wasu dubbai da suka rasa muhallansu suka koma zama a cikin tantuna ko kwantainoni.

Girman asarar

Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya, Suleman Soylu, ya sanar cewa ’yan kasarsa 45,968 da ’yan kasar Siriya 4,267 da ke gudun hijira a Turkiyya ne suka rasu a girgizar kasar.

Girgizar kasar ta kuma rusa gine-gine akalla 214,000, yawancinsu a yankin Hatay da kuma Kahraramanmaras.

Wadanda suka rasa muhallansu sun haura mutum miliyan 14, wato mutum daya a cikin kowane mutum shida da ke kasar.

Har yanzu ma’aikatan ceto na ci gaba da aikin kwashe baraguzai a yankunan da aka samu iftila’in, wanda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce ya tilasta tashin mutum miliyan 3.3 daga yankunan da abin ya faru.

Ya bayyana cewa an sama wa mutum miliyan 1.4 daga cikinsu  matsuguni a cikin tantuna, wasu 46,000 kuma a cikin kwantainoni, ragowar kuma a dakunan kwanan dalibai a makarantu da masaukan bakin gwamnati.

Takaici

Jama’ar kasar na ci gaba da bayyana takaicinsu bisa yadda suke ganin matakan da gwamnatin kasar take dauka kan matsalar.

Sai dai Shugaba Erdogan ya danganta rashin saurin ayyukan agajin a kan tsananin hunturu da ya sa dusar kankara da ta rufe tituna, gami da lalacewar hanyoyi da filayen jiragen sama a sakamakon iftila’in.

A wasu yankuna irin su Adiyaman, mutane sun fusata kwarai da gwamnati, domin sai da suka yi kwanaki bayan girgizar kasar suna amfani da hannuwansu wajen ceto ’yan uwansu da suka makale a cikin baraguzai ko gini ya danne su, kafin sojoji da ma’aikatan ceto su kawo musu dauki.

Wasu daga cikinsu sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a kan idanunsu ’yan uwansu da gini ya danne suka rika mutuwa, saboda rashin kayan aikin da za a fasa kankare a ciro su.

Bayan shan suka daga al’ummar kasar kan yadda gwamnati ke daukar mataki kan lamarin, Shugaba Erdogan ya amsa laifin gazawar gwamnatin tare da neman afuwarsu.

A lokacin da ya ziyarci wani yanki da aka samu girgizar kasar, Mista Erdogan ya ce, “Abu ne mai wuya a ce an yi wa iftila’i mai girma haka shirin ko-ta-kwana.”

Sai dai jam’iyyun adawa na zargi hukumomin gwamnati da tafiyar hawainiya wajen gudanar da aikin ceton.

Ita kanta kungiyar agaji ta Red Crescent ta sha suka, saboda sayar da tantuna ga wadanda iftila’in ya raba da muhallansu, maimakon agaza musu da tantunan.

Babu wani jami’in gwamnati da ya amsa mas’uliyyar jinkirin aikin agajin ko ya ajiye aikinsa, sai dai ana zargin ’yan kwangila da kamfanonin gine-gine da saba ka’idojin gini, ganin yadda gine-gine da dama suka yi mummunar rugujewa a girgizar kasar.

Kawo yanzu hukumomin Turkiyya na tsare da mutum sama da 200 ciki har da ’yan kwangilar gine-gine.

Daga cikinsu har da wadanda aka kama a filin jirgin sama suna shirin barin kasar.

Darajar asarar

Bankin Duniya ya kiyasta cewa asarar da Turkiyya ta yi a sakamakon girgizar kasar ya kai na Dala biliyan 34, banda na gine-gine.

Bankin ya ce kudin ya kai kashi hudu cikin 100 na kayayyakin da kasar ta samar a cikin gida a shekarar 2021, sannan abin da za a kashe wajen sake gine-gine na iya ninka shi sau biyu.

Ko kafin girgizar kasar Turkiyya na fama da matsalar hauhawar farashin kaya da kuma faduwar darajar kudinta, Lira, a kasuwar canji.

Ga shi babban zaben kasar na kara matsowa, kuma Shugaba Erdogan ya yi alkawarin a cikin shekara guda zai samar da gidaje ga mutum miliyan daya daga cikin wadanda suka rasa gidajensu a girgizar kasar.

A kusan shekara 20 na mulkin Erdogan, gwamnatinsa na bugun kirji da zamanantar da Turkiyya, a bangaren gine-gine, inda ta gina katafarun tituna da hanyoyi da gadoji da hanyoyin karkashin kasa.

Bankin Raya Kasashen Turai ya yi hasashen cewa Turkiyya za ta iya samun riba mai yawa a wajen ayyukan sake gina kasar bayan girgizar kasar.

Bankin ya ce, “Karuwar amfanin da za a samu daga ayyukan sake gina kasar za ta kawar da illolin da aka samu a sakamakon iftila’in.”

Tasiri a siyasa

Duk da girgizar kasar da aka samu, Erdogan ya sanar cewa, hukumar zaben kasar za ta gudanar da zaben ’yan majalisar dokoki kamar yadda aka tsara da farko a ranar 14 ga watan Mayu.

A watan Fabrairu, shugaban ya ayyana dokar ta-baci na tsawon wata uku a daukacin yankunan da aka samu girgizar kasar, matakin da ya sa aka yi tunanin zai dage zaben.

Sai dai sanarwar da ya yi a makon jiya cewa za a yi zaben yadda aka tsara bai fayyace tanadin da aka yi domin wadanda suka yi kaura daga yankunansu su samu kada kuri’a ba.

Gudanar da zaben dai na da matukar muhimmanci ga Mista Erdogan, wanda ke jagorantar kasar tun daga shekarar 2003, farko a matsayin fira minista, daga baya kuma a matsayin shugaban kasa.

Girgizar kasar ta kawo jinkiri ga jam’iyyun adawar Turkiyya wajen sanar da dan takararsu na hadin gwiwa, wanda ake sa ran za su sanar a ranar Litinin.

Ana hasashen dan takarar da za su ayyana shi ne Kemal Kilicharoglu, shugaban babbar jam’iyyar adawa ta CHP.

Sai dai kuma shugaban jam’iyyar adawa ta ’yan kishin kasa ya nuna tsananin adawarsa ga takarar Kemal Kilicharoglu.